Baturiya Ta Fallasa Masoyinta Dan Najeriya Wanda Ya Barta Da Ciki Don Auren Yar Najeriya
- Wata baturiya ta fallasa masoyinta dan Najeriya wand ya koma gida Najeriya don ya auri wata daban
- A cewarta, ya barta a lokacin da take dauke da cikin mako 39 kuma kwana daya bayan cikarsu shekaru 5
- Matar wacce ta karaya ta saki hotunanta tare da mutumin lokacin da abubuwa ke tafiya daidai kuma mutane sun yi martani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata baturiya, Jennaa_xxoo, ta caccaki masoyinta dan Najeriya kan auren wata yar Najeriya da ya yi a boye.
A wata wallafa da ta yi a TikTok, Jennaa, ta fallasa mutumin bayan ta shiga yayin da mata ke yi na fadin abun da ya faru bayan sun amsa sakon waya.
Jennaa ta ce tana da cikin mako 39 lokacin da ya yi watsi da ita
A cewar Jennaa, mutumin ya aika mata sako ta soshiyal midiya a 2018 kuma daga nan ne suka fara soyayya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai kuma, ya koma gida Najeriya don auren wata daban, Jennaa ta ce ya barta lokacin da take dauke da cikin wata tara kuma kwana daya bayan sun yi cikarsu shekaru biyar tare. Ta yada hotunan masoyin nata tare da amaryarsa.
Jennaa ta tuno da lokacin da abubuwa ke tafiya daidai
A wata wallafar da ta sake yi a TikTok, Jennaa ta yada hotunan mutumin, danta, da ita kanta yayin da take tuna lokacin da abubuwa ke tafiya daidai.
Jennaa ta ce ko da yake abun akwai ciwo sosai, har yanzu tana girmama dan kankanin lokacin da suka yi rayuwa a matsayin iyali.
"Koda yake akwai radadi mai zafi a bayan idanu da murmushina, har abada zan cigaba da girmama dan kankanin lokacin da muka sake ji tamkar iyali, ta rubuta.
“Tana Ba Da Jikinta Don Samun Maki a Makaranta”: Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Kwanaki Kadan Kafin Bikinsu
Kalli bidiyonta a kasa:
Mutane sun karfafawa Jennaa gwiwa kan lamarinta
shoumhvew3d ta ce:
"Ina mai baki hakuri da wannan hali da kika shiga wanda ya dace zai zo kuma ya nuna maki soyayya ta gaskiya."
PhayvorJay23 ta ce:
"Ina mai baki hakuri yar'uwa..yaronki na da kyau...Ubangiji zai kawo wani na musamman da zai tsaya har abada."
Stargirl ta ce:
"Kina da kyau da karfin zuciya yarinya!!! Kada ki bari kowani da namiji yasa ki kaskantar da kanki❤️❤️… babban rabo na nan tafe."
Dan ministan tsaro ya angwance da kyakkyawar matarsa
A wani labarin kuma, mun ji cewa Ahmad, dan ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru, ya angwance da sahibarsa, Zainab Nasidi, a wani kasaitaccen biki da aka yi a makon nan.
An daura auren Ahmad da Zainab a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, a babban masallacin Juma'a na Isyaka Rabi'u da ke garin Kano.
Asali: Legit.ng