Tsohon Sakataren Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje Daga Kano, Dakta Al-Adam Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Tsohon Sakataren Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje Daga Kano, Dakta Al-Adam Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An shiga jimami yayin da aka yi babban rashi a jihar Kano a jiya Asabar 2 ga watan Satumba na wani tsohon dan siyasa
  • Marigayin Dakta Muhammad Bello Al-Adam ya rasu ne a kasar Indiya bayan fama da gajeriyar jinya
  • Dakta Bello kafin rasuwarshi ya yi aiki a banki da kuma ma'aikatar harkokin kasashen waje kafin ya tsunduma harkokin siyasa

Jihar Kano - Tsohon sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje, Dakta Muhammad Bello Al-Adam ya riga mu gidan gaskiya.

Dakta Bello ya rasu ne a jiya Asabar 2 ga watan Satumba bayan fama da gajeriyar jinya a kasar Indiya.

Dakta Bello Al-Adam daga Kano ya riga mu gidan gaskiya a kasar Indiya
Marigayi Dakta Bello Al-Adam Ya Rasu A Kasar Indiya. Hoto: PM News.
Asali: UGC

Wani babban rashi aka yi a Kano?

Yayin sanar da rasuwarshi, 'yan uwan marigayin sun ce za a bayyana lokacin sallar jana'izarshi da zaran an dawo da gawar zuwa gida Najeriya.

Kara karanta wannan

Halin Yunwa: Dalibi Ya Rasa Ransa Kan Zargin Rashin Wadataccen Abinci Mai Gina Jiki A Wata Makaranta Da Ke Jihar Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayin wanda asali dan jihar Kano ne ya taba koyarwa a makarantar alkalai a Shahuci ta jihar Kano kafin komawa ma'aikatar harkokin kasashen waje.

Daga bisani Dakta Bello ya tsunduma a harkokin banki kafin ya yi ritaya ya koma kasuwanci da kuma siyasa, PM News ta tattaro.

Bello Al-Adam ya kasance mai taimakon jama'a ta ko wane hali inda hakan nema ya sa shi neman takarar gwamna a jihar a jam'iyyar UNCP a 1998.

Marigayin ya yi gwagwarmaya a Kano da kuma Najeriya

Yayin gwagwarmayar siyasa, ya zama mamba a jam'iyyun APP da ANPP da CPC sai kuma APC inda ya kasance daga cikin masu ruwa da tsaki a yayin kamfe na Tinubu/Shettima a 2023.

Ya kasance majibincin kungiyar Tinubu People's Network (TPN) yayin yakin neman zaben shugaban kasa a 2023, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekara 20 Ya Kashe Mahaifinsa Don Asirin Neman Abin Duniya, Bayanai Sun Fito

Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Kwamishiya A Jihar Kano Rasuwa

A wani labarin, Allah ya yiwa tsohuwar kwamishiniya a ma'aikatar harkokin mata ta jihar Kano, Barr. Zubaida Damakka Abubakar, rasuwa.

Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, a wani asibiti dake a birnin tarayya Abuja.

Za a gudanar da jana'izar marigayiyar a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli, a gidansu dake a Unguwar Gwammaja cikin birnin Kano, da karfe 9:00 na safe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.