Akwai Yiwuwar Tinubu Ya Fatattaki Wadanda Buhari Ya Ba Mukami Daf da Barin Mulki
- Muhammadu Buhari ya yi ta nade-naden mukamai har zuwa lokacin da awanni su ka rage masa a ofis
- Ana tsoron Bola Ahmed Tinubu zai iya korar wadanda aka nada, ya kawo wasu mutanensa dabam
- Tinubu ya nada sababbin hafsun sojoji, hadimai da ministoci kuma ya kama hanyar canza jakadu
Abuja - A farkon 2021 ne Muhammadu Buhari a lokacin ya na shugaban kasa, ya rantsar da Jakadun Najeriya da za su wakilce ta a kasashen waje.
Bayan yin kusan shekaru biyu a ofis, sai aka ji sanarwa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci jakadun su dawo gida, ya yi wa dukkansu kiranye.
Abin da hakan ya nuna shi ne ana shirin nada sababbin Jakadun Najeriya a kasashen kataren.
Daga lokacin da ya hau mulki zuwa yanzu, sabon shugaban Najeriya watau Bola Tinubu ya nada hadimai, hafsun sojoji da ministocin gwamnatinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mukaman Buhari a mintin karshe
Jaridar Punch ta ce ba abin mamaki ba ne Tinubu ya tsige wasu daga cikin wadanda Muhammadu Buhari ya nada a lokacin da wa’adinsa ya zo karshe.
Ana saura makonni a nada sabon shugaban kasa, AIG Garba Baba-Umar (mai ritaya) ya zama mai bada shawara a ofishin ministan harkokin ‘yan sanda.
Gwamnatin Buhari ta nada mukamai a ma’aikatun muhalli, kiwon lafiya, ilmi, harkokin jiragen sama har zuwa lokacin da awanni su ka rage mata.
A haka ne Bello Maigari da Dr Gambo Aliyu su ka zarce a hukumar asusun caca da ta NACA, kuma aka nada Garzali Abubakar ya rike hukumar tarayya.
Kusan sai bayan Tinubu ya zama shugaban kasa aka ji Sha’aban Sharada ya zama shugaban hukumar kula da almajirai da yaran marasa zuwa makaranta.
Tinubu ya fara yin waje da wasu
Wasu daga cikin wadannan da aka ba mukami a mintin karshe sun rasa kujerunsu. Na baya-baya shi ne Dr. Bashir Gwandu wanda aka kora daga NASENI.
Akwai yiwuwar wasu su biyo Gwandu, gwamnatin tarayya ta maye gurbinsu da wadanda ta ke ganin sun fi dacewa ko da wa’adinsu bai kare ba tukuna.
Nade-naden mukami a Kano
Ku na da labari Abba Kabir Yusuf ya amince da karin nadin mukamai sama da 100, ya nada wadanda za su rika taimaka masa a dandalin sada zumunta.
Baya ga haka, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sunayen wasu mutum 57 da za su taya Gwamnan jihar Kano aiki a bangarori dabam-dabam.
Asali: Legit.ng