Shugaban Kasa Bola Tinubu: Cikakkun Sunayen Sabbin Hafsan Sojoji, IGP Da Shugaban Kwastam

Shugaban Kasa Bola Tinubu: Cikakkun Sunayen Sabbin Hafsan Sojoji, IGP Da Shugaban Kwastam

  • Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi gagarumin sauye-sauye yayin da ya amince da yi wa shugabannin hafsan soji, IGP da wasu da dama ritaya.
  • Shugaban kasar ya kuma sanar da magadan shugabannin sojoji, IGP, shugaban Kwastam da sauransu wadanda aka nemi su gaggauta kama aiki
  • Lamarin ya kuma shafi jami'an soji a fadar shugaban kasa da kuma shugabannin tsaro a babban birnin tarayya

Aso Villa, Abuja - Makonni uku da kama aikin shugabancin kasa, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da yi wa shugabannin tsaro ritaya nan take a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.

Sauye-sauyen ya kuma shafi Sufeto Janar na yan sanda, manyan masu ba da shawara kan tsaro da kuma kwanturola janar na Kwastam yayin da aka sanar da madadinsu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

Asiwaju Bola Tinubu
Shugaban Kasa Bola Tinubu: Cikakkun Sunayen Sabbin Hafsan Sojoji, IGP Da Shugaban Kwastam Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shugabannin tsaro nawa Shugaban kasa Tinubu ya nada?

Sai dai kuma, an tattaro cewa sabbin shugabannin tsaron, IGP, da kwanturola janar na kwastam za su yi aikin rikon kwarya ne har zuwa lokacin da za a tabbatar da su daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Willie Bassey, daraktan labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya saki.

Ga jerin sunayen, da jawaban sabbin shugabannin tsaro, IGP da sauransu.

  1. Mallam Nuhu Ribadu Mai ba kasa shawara kan tsaro
  2. Manjo Janar C.G Musa shugaban ma'aikatan sojoji
  3. Manjo T. A Lagbaja Babban hafsan soji
  4. Rear Admirral E. A Ogalla Babban hafsan sojin ruwa
  5. AVM H.B Abubakar Babban hafsan sojin kasa
  6. DIG Kayode Egbetokun Mukaddashin shugaban yan sanda
  7. Manjo Janar EPA Undiandeye Shugaban hukumar leken asiri

Sauran jami'an tsaro da shugaban kasa Tinubu ya nada.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Girgiza Najeriya Cikin Makonsa Na 3 a Matsayin Shugaban Najeriya

  1. Canal Adebisi Onasanya - Kwamandan bataliyar tsaro
  2. Laftanal Kanal Moshood Abiodun Yusuf - Kwamandan bataliyar tsaron runduna ta 7 da ke Asokoro a Abuja
  3. Laftanal Kanal Auwalu Baba Inuwa - Kwamandan bataliyar tsaron runduna ta 177 da ke jihar Nasarawa
  4. Laftanal Kanal Mohammed J. Abdulkarim - Kwamandan bataliyar tsaron runduna ta 102, da ke Suleja a jihar Neja
  5. Laftanal Kanal Olumide A. Akingbesote - Kwamandan bataliyar tsaron runduna ta 176 da ke Gwagwalada a Abuja

Shugaban kasa Tinubu ya kuma nada sabbin jami'an soji a fadar shugaban kasa.

Sabbin sojojin fadar shugaban kasa

  1. Manjo Isa Farouk Audu - Babban jami’in yaki da makamai na fadar shugaban kasa
  2. Kyaftin Kazeem Olalekan Sunmonu - Mataimakin kwamandan yaki da makamai na fadar shugaban kasa
  3. Manjo Kamaru Koyejo Hamzat - Kwamandan dakarun soji masu tattara bayanan sirri a fadar shugaban kasa
  4. Manjo TS Adeola - Kwamandan kula da Makamai na fadar shugaban kasa
  5. Lt. A. Aminu - Mataimakin kwamandan kula da makamai na fadar shugaban kasa

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Mai Kudin Afrika, Aliko Dangote a Aso Rock

Duba wallafar a kasa:

Majalisar shari'a ta ba da shawarar nada ma'aikatan shari'a 37 a mukamai daban-daban

A wani labari na daban, mun ji cewa majalisar harkokin shari’a a Najeriya (NJC) ta bayar da shawarar nada mutane tara a kotun daukaka kara.

Hakazalika ta bayar da shawarar nada wasu ma'aikatan shari'a 27 a kan wasu mukamai, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel