Wike Ya Tsokano Fada, Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Kai Minista Gidan Yari
- Mohammed Ibrahim Kamba ba zai hakura da gininsa da hukumar FCTA ta rugurguza a Abuja ba
- Lauyan ‘dan kasuwar ya fitar da jawabi, ya musanya ikirarin FCTA na yin gini a filin wani mutumi
- Alhaji Kamba ya ce shi ya mallaki filin da ake ta rikici a kai, kuma har kotu ta taba ba shi gaskiya
Abuja - Mohammed Ibrahim Kamba, ‘dan kasuwa ne a Abuja wanda ya dauki alwashin ganin ministan birnin tarayya, Nyesom Wike a kurkuku.
Kamar yadda Daily Trust ta fitar da labari dazu, Alhaji Mohammed Ibrahim Kamba ya ce ministan zai kare a gidan yari kuma zai yi karar jami’in FCTA.
‘Dan kasuwan zai shigar da karar Darektan kula da cigaban gine-gine a hukumar FCTA, a cewarsa jami’in ya tsallake iyakarsa da ya rusa masa gini.
Abuja: Bayanin da FCTA ta yi
A farkon makon nan aka ji FCTA ta na bayanin abin da ya jawo aka rusa wani katafaren gini wanda shi Mohammed Ibrahim Kamba ya mallaka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A bayanin da ‘dan kasuwar ya yi, ya karyata zargin da ake yi masa na taba filin wani dabam. Hakan na zuwa ne bayan an rusa kasuwar Dare kwanan nan.
Lauyan 'dan kasuwa ya kalubalanci Wike
Jawabin ya fito ne ta bakin lauyansa, Okechukwu C. Uju-Azorji yake cewa za su yi karar ministan bisa zargin raina hankali da wulakanta kotun tarayya.
Lauyan ya hakikance a kan cewa tun farko filin da ake magana na wanda su ka saya a hannunsa ne, wanda ya gina karamin gidan tarbar baki watau BQ.
A cewar lauya, an yi shekaru 25 da wannan karamin gida a filin, kafin ya saida shi a shekarar 2019, daga nan shi kuma Kamba ya saye gidan a hannunsa.
“Sai Alhaji Mohammed Ibrahim Kamba ya saye filin a hannun asalin wanda aka ba, Oyebade Lipede.
"Da wanda mu ke karewa ya fara gina filin, har da gyara gidan bakin, sai wani lauya a Abuja ya shigar da kara a kan shi a wata kotu a Area I a Abuja.
"Lauyan ya yi zargin an shiga filin da babu hurumi, ya na cewa filin na Sarkin Egba, Marigayi Oyebade Lipede ne, amma aka yi watsi da karar a 2020."
- Okechukwu C. Uju-Azorji
A maimakon ayi abin da ya dace, rahoton ya ce sai FCTA ta biyewa zancen wancan lauya, saboda haka aka shirya yin shari’a da ministan da hukumar.
Wike ya zama Ministan Abuja
A jiya aka ji sabon Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa bai taba hango kansa kan wannan kujerar gwamnatin tarayya da yake kai ba.
Jigon na PDP ya ce ya sha mamaki a lokacin da ya samu labarin mukamin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ba shi da aka raba ministoci.
Asali: Legit.ng