Tinubu Ya Fadawa Wike Abin da Yake So a Abuja - Idan Na Nemi Fili Ka da a Yanka Mani

Tinubu Ya Fadawa Wike Abin da Yake So a Abuja - Idan Na Nemi Fili Ka da a Yanka Mani

  • Bola Ahmed Tinubu bai bukatar ya nemi kyautar fili daga wajen babban ministan birnin tarayya
  • Shugaban kasar Najeriyan ya fadawa Nyesom Wike cewa ba zai nemi a yanka masa fuloti a Abuja ba
  • Abin da Shugaba Bola Tinubu yake so ministan ya yi shi ne ya kammala aikin jirgin kasan birnin

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya karasa aikin jirgin kasan garin Abuja.

Legit.ng Hausa ta lura Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya samu halatar taron kungiyar lauyoyi na kasa watau NBA wanda aka kaddamar a jiya.

Da ya ke magana wajen bude taron, The Cable ta ce shugaban kasa ya ce zai so a kammala aikin dogon Abuja, domin al’umma su amfana.

Kara karanta wannan

Ba Za Ta Yi Wu Ba: Tinubu Ya Bayyana Tsari 1 Na Buhari Da Ba Zai Cigaba Da Shi Ba

Bola Tinubu da Nyesom Wike
Shugaban kasa da Nyesom Wike a Fatakwal Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu: Jirgin kasan Abuja ya na da amfani

Bola Tinubu ya ce shi kan shi zai so ya shiga jirgin, saboda haka ya bukaci sabon ministan ya yi bakin kokarinsa domin ganin an kammala.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rahoton da aka samu daga Nairaland, an ji yadda shugaban Najeriyan ya jaddadawa tsohon gwamnan na Ribas muhimmancin dogon.

"Ina iya ganin babbanmai masaukin bakinmu, uban gidan Abuja. Ka dage da haka, ina so in shiga jirgin kasan ka a tuka ni.
Idan na tambaye ka kyautar fili, ka da ka ba ni, amma ka samar da jirgin kasan cikin birni domin dinbin al’ummar Najeriya."

- Bola Tinubu

Wike zai biya mazauna Abuja hakkokinsu

Tuni har ministan ya tsaida wa’adi domin a biya mutane hakkokinsu domin su bar gidajensu da ke wuraren da titin jirgin zai bi.

Kara karanta wannan

Ana Mulkin 'Yan Koyo: Shehu Sani Ya Jero Wadanda Ya Kamata Tinubu Ya Nada Ministoci

Wike ya bayyana haka a ranar Laraba da ya ziyarci tashar jirgin kasa da ke Idu da filin jirgin sama domin ya ganewa idanunsa.

Ministan ya zauna da Festus Keyamo domin ganin yadda za a sallami mazauna da gidajensu su ka fado ta yankin da titin jirgin zai bi.

Nyesom Wike ya zo da shirin aiki

Nyesom Wike ya shiga ofis a makon da ya gabata, ya kama shirin aiki babu kama hannun yaro, ya ce zai dawo da darajar Abuja.

Tun a lokacin aka aji sabon ministan tarayyar ya fadawa ma’aikatan da ba su da niyyar aiki a birnin Abuja su canza ma’aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel