“Za a Iya Korarka Daga PDP” ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Caccaki Nyesom Wike

“Za a Iya Korarka Daga PDP” ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Caccaki Nyesom Wike

  • An fadawa Nyesom Wike bai fi karfin a hukunta shi ba, tun ba shi ya mallaki Jam’iyyar PDP ba
  • Wannan shi ne ra’ayin Dele Momodu, wanda ya zama kakakin Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa
  • ‘Dan siyasar ya yi wa Wike raddi, ya na mai karyata wasu abubuwan da ya fada a hirar da aka yi shi

Abuja - Gawurtaccen ‘dan jarida kuma ‘dan siyasa, Dele Momodu ya tunawa Nyesom Wike cewa jam’iyyar adawa ta PDP ba mallakinsa ba ce.

Tsohon ‘Dan takarar shugaban kasar ya yi magana ne a matsayin raddi ga sabon ministan Bola Tinubu, This Day ta fitar da rahoton nan a yau.

Cif Dele Momodu ya fadawa Nyesom Wike akasin abin da yake tunani, ya ce za a iya ladabtar da tsohon gwamnan na Ribas idan har ya yi laifi.

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

Nyesom Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Nyesom Wike ya shirga karya?

Ganin Wike ya na cewa babu wanda ya isa ya dakatar da shi daga PDP, sai kakakin kwamitin yakin zaben Atiku/Okowa ya maida masa martani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin da Momodu ya fitar a jiya, ya bayyana cewa wasu abubuwan da Wike ya fada a hirar da aka yi kwanan nan da shi, duk karyayyaki ne.

‘Dan siyasar ya zargin ministan tarayyar da Gadara da kin fadin gaskiya a game da maganar takarar shugaban kasa da PDP ta bari a yankin Arewa.

An rahoto Momodu na zargin Wike da fakewa da tsaida ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa daga Kudu bayan Atiku Abubakar ya ki dauko shi.

Wike bai fi karfin doka a PDP a

PDP ta cika shekaru 25 a Najeriya, ‘dan jaridar ya ce ministan bai cikin wadanda aka kafa Jam’iyyar a 19998 da su saboda haka za a iya hukunta shi.

Kara karanta wannan

Wike: Hadimin Atiku Ya Fadi Lokacin Da PDP Za Ta Kori Ministan Abuja

Jim kadan bayan an yi hira da Wike, Momodu ya ce ya kira Seun Okinbaloye ya fada masa da ya na Najeriya, da nan ta ke ya maida masa martani.

Independent ta ce tsohon gwamnan ya nemi Atiku ya ba shi ma’aikata mai tsoka idan an ci zabe, da bai samu hakan ba ya koma wajen Bola Tinubu.

A cewar Momodu, babu inda doka ta ce dole daga Arewa za a fito daga ‘dan takaran PDP a zaben 2023, yake cewa kwamiti ya bar kofar tikitin ne a bude.

Jawabin ya karyata batun cewa Tinubu ya bukaci gwamnonin adawa su kawo wadanda za a ba ministoci, ya ce har ‘yan G5 ba su tsira da komai ba.

Mohammed Ibrahim Kamba v Wike

Mohammed Ibrahim Kamba ya musanya zargin da FCTA ta ke yi masa, ya ce shi ne saye filin da aka rusa masa gini a kai a hannun asalin mai fulotin.

An ji labari lauyan 'dan kasuwar ya na cewa an yi watsi da karar da aka kai shi a 2020, ya na neman zuwa kotu da Nyesom Wike da hukumar FCTA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng