Daga Kiss, Amarya Ta Yi Wa Ango Fentin Fuska Da Kwalliyarta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Yadu
- Wani bidiyo da ya yadu ya nuno lokacin da wani ango da amarya suka sumbaci junansu a wajen shagalin bikinsu
- A cikin bidiyon, an gano angon dauke da kwalliya a fuska da labbansa bayan ya sumbaci amaryar tasa
- Mahalarta bikin sun fashe da dariya bayan angon ya janye daga amaryar tare da daga fuskarsa don kallon jama'a
Wani bidiyon shagalin biki ya nuna wani ango yana sumbatar amaryarsa cike da shauki.
Sai dai bayan sun gama sumbatar junansu, an gano fuskar angon ta yi dama-dama da hodar amaryar.
A cikin bidiyon angon ya sumbaci amaryar tasa sosai ba tare da sanin cewa kwalliyarta za ta yadu a nasa fuskar ba.
A lokacin da ya janye daga jikin matar tasa tare da daga fuskarsa, sai mahalarta bikin suka fashe da dariya bayan sun ga abun da kwalliyar ta yi wa fuska da labbansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bidiyon shagalin biki ya nuno yadda amarya ta fenta fuskar ango da kwalliyarta
Mutumin ya dauki abun cikin sauki yayin da ya maida martani da dan murmushi. Labbansa sun koma kalar kwalliyar matarsa.
Hakazalika goshinsa ma ya kwashi kwalliyar, yayin da ya koma kalar hodar amarya.
Bidiyon ya yadu bayan shafin @yabadeyment ya wallafa shi a manhajar X.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani ga bidiyon amaryar da ta sumbaci ango a wajen biki
@YawMensah_ ya ce:
"Mutumin ya koma dan barkwanci."
@auntypeepee ta ce:
"Haka ma ake sumbata? Allah ya kyauta."
@EruditeArc ya yi martani:
"Ya kamata na nadi bidiyon nan."
@Max_J619 ya ce:
"Kwalliyar naira miliyan 5."
Matar aure ta sume bayan gwajin DNA ya nuna ba mijinta ne uban dansu ba
A wani labari na daban, mun ji cewa wata uwa ta shiga tsananin damuwa bayan sakamakon gwajin DNA ya tabbatar da cewar mijinta ba shine ainahin uban danta ba.
Da take jinjina sakamakon, matar wacce ta karaya ta yanke jiki ta fadi a cikin wani bidiyo mai tsuma rai wanda 'The Closure DNA Show' ya wallafa.
Gwajin DNA ya nuna 0% Yayin da yake karanto sakamakon da babban murya, mai gabatarwar ya sanar da cewar yiwuwar mutumin na zama mahaifin 'dan ya kasance 0% kamar yadda gwajin kwayoyin halittar ya tabbatar.
Asali: Legit.ng