Kotun Musulunci Ta Daure Wani A Jihar Kano Kan Satar Shanu Har Na Naira Dubu 700
- Kotun Shari'ar Musulunci da ke Kano ta daure wani mutum shekara guda a gidan kaso kan zargin sata
- Wanda ake zargin, Usaini Hamisu mai shekaru 45 ya saci shanun ne da su ka kai Naira dubu 700
- Alkalin kotun daga bisa ya umarci daure Hamisu na tsawon shekara daya tare da zabin biyan tara Naira dubu 50
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Kotun Shari'ar Musulunci da ke Kano ta daure wani mutum shekara guda a gidan kaso kan zargin satar shanu guda biyu.
Wanda ake zargin da ke zaune a unguwar Dorayi, Usaini Hamisu mai shekaru 45 ya saci shanun ne da su ka kai Naira dubu 700.
Meye alkalin kotun ya ce a Kano?
Alkalin kotun, Mallam Nura Yusuf Ahmed ya daure Hamisu shekara daya a gidan kaso tare da zabin biyan kudin tara Naira dubu 50.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da alkalin kotun ya umarci jami'an 'yan sanda da su dawo da shanun ga mai su.
Tun farko dan sanda mai gabatar da kara, Mista Aliyu Abideen ya shaida wa kotu cewa wani mutum ya kawo kara a ranar 24 ga watan Agusta ofishin 'yan sanda na Zango.
Ya ce wanda ya shigar da karar shi ne Garba Audu daga kauyen Kazawa cikin karamar hukumar Minjibir da ke cikin jihar Kano.
Abideen ya ce a ranar kuma da misalign karfe 2:00 na dare wanda ake karar ya je gidan wanda ke kara tare da sata masa bujumaye guda biyu da kudinsu ya ka Naira dubu 700, cewar Tribune.
Ya ce an kama wanda ake zargin a kauyen Rangaza a lokacin da ya ke kokarin tserewa da shanun.
Meye wanda ake zargin ya ce a kotun Kano?
Yayin bincike, Hamisu ya tabbatar cewa duk lokacin da ya je sata ya na amfani da layu da sanda da kuma farin kyalle yadda shanun ba za su yi ihu ba.
Hamisu ya kara da cewa wannan asirin da zai yi lokacin satar zai sa mai su ya yi ta bacci har sai ya gama abinda zai yi tukun, Phenomenal ta tattaro.
Abideen ya ce:
“Bokan da ya masa asirin ya ce idan ta karye zai fara zufa, inda ya wanda ake zargin ya tabbatar cewa asirin ne ya karye shi yasa aka kama shi.”
Wanda ake zargin ya amince da dukkan tuhume-tuhumen da ake a kansa na satar shanu na Naira dubu 700.
Kotun Musulunci A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Wata 15 A Gidan Kaso
A wani labarin, kotun shari'ar Musulunci ta gurfanar da wani lauyan bogi mai suna Zaharaddin Sani Maidoki a gaban kotun shari'ar Musulunci bisa zargin yaudara da cin amana.
Karauniya Yayin Da Kotu Ta Daure Mutum 2 Kan Zargin Satar Kayan Motocin Dangote Na N976,715, Ta Yi Bayani
Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan kaso.
Asali: Legit.ng