Wata Mata Ta Fadi Sumammiya Bayan Gwajin DNA Ya Tabbatar Ba Mijinta Bane Uban Danta
- Wata mata ta sharbi kuka da hawaye bayan sakamakon gwajin DNA ya nuna cewa mijinta na ta rainon dan da ba nasa bane
- Matar da ke cikin damuwa ta fice daga wajen da ake hira da ita a Talbijin kafin ta yanke ciki ta fadi saboda kaduwa
- Sakamakon gwajin ya nuna babu ko digon kwayar halittar mijin a tattare da dan nata wato dai ya nuna 0%
Wata uwa ta shiga tsananin damuwa bayan sakamakon gwajin DNA ya tabbatar da cewar mijinta ba shine ainahin uban danta ba.
Da take jinjina sakamakon, matar wacce ta karaya ta yanke jiki ta fadi a cikin wani bidiyo mai tsuma rai wanda 'The Closure DNA Show' ya wallafa.
Gwajin DNA ya nuna 0%
Yayin da yake karanto sakamakon da babban murya, mai gabatarwar ya sanar da cewar yiwuwar mutumin na zama mahaifin 'dan ya kasance 0% kamar yadda gwajin kwayoyin halittar ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A takaice, muna cewa yallabai ba kaine uban annan 'da ba ko shakka babu," ya jadadda.
Bayan an karanto sakamakon, matar ta cire lasifika daga jikin rigarta kafin ta wuce daga wajen sannan ta yake jiki ta fadi a kasa.
An gano wata mata tana kokarin kwantar wa matar da ke sharban kuka da hankali.
Burin matar ya rushe
Ga dukkan alamu, matar ta kwallafa a ranta cewa mutumin ne uban danta, kawai sai ga shi komai ya ruguje a kanta.
A daya bangaren, mutumin da ke cike da bakin ciki ya zauna sannan ya dunga kallon diramar da ke faruwa ba tare da ya furta komai ba.
Shakka babu, tambayar da ke yawo a zuciyarsa ta samu amsa, watakila ba wanda ya yi burin samu ba.
Hanyar da aka bi don samun karin haske, ya wargaza dangantakar su kuma ya rura wutar damuwa tsantsa.
Wata mata ta haifi yara tara, ta ce akwai karin wasu tafe
A wani labari na daban, mun ji cewa wata yar kasar China mai suna Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong sun ja hankalin jama'a bayan sun haifi yara tara a cikin shekaru 13 da suka gabata.
A cewar Mothership, matar wacce ke ganiyar shekaru 30 da doriya ta haifi diyarta ta farko a 2010.
Asali: Legit.ng