Ana Ta Tafka Muhawara Game Da Yadda Aka Samar Da Jariri Daga Kwayoyin Halittan Mutane 3 a Birtaniya

Ana Ta Tafka Muhawara Game Da Yadda Aka Samar Da Jariri Daga Kwayoyin Halittan Mutane 3 a Birtaniya

  • An samar da wani jinjiri a ƙasar Birtaniya daga ƙwayoyin halittar mutane uku ta amfani da wata sabuwar hikima ta dashen 'mitochondria' (MDT)
  • Sabuwar hikimar dai a cewar masana, za ta taimaka wajen magance matsalolin da yara ke gadowa irinsu matsalolin ƙwaƙwalwa, zuciya da makanta
  • Wannan hikimar ta ƙunshi gauraya ƙwayoyin halittar iyayen jinjirin na ainihi, da kuma wani kaso ɗan kaɗan na wani lafiyayyen mutum na daban

Birtaniya - A karon farko, masana kimiyya sun samar da wani jinjiri a ƙasar Birtaniya daga ƙwayoyin halittar mutane uku a cewar gidan talabijin na Al Jazeera.

An dai samar da jinjirin ne ta hanyar amfani da wata sabuwar hanyar haihuwa da aka yiwa laƙabi da 'mitochondrial donation treatment' (MDT) wacce ake sa ran za ta taimaka wajen hana yaro kamuwa daga cututtuka irin na gado.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar N22bn

Jaririr UK
Masaniyar kimiyya, Jariri. Hoto: Al Jazeera, BBC
Asali: TikTok

Ana cirar lafiyayyar 'mitochondria' daga mutum na ukun

Masanan sun bayyana cewa kaso mafi yawa daga ƙwayoyin halittar da akai amfani da su duk na ainihin iyayen jinjirin ne, a yayin da kuma wani kaso da bai wuce 0.1% ba ne za a karɓa daga wata matar ta daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a ciri kwayar halittar 'mitochondria' ne daga matar. 'Mitochondria' ce dai ke da alhakin sarrafa abinci domin amfanin ƙwayoyin halittar cikin jikin ɗan adam.

Sun ce 'mitochondria' da take da matsala kan iya sabbaba ciwon ƙwaƙwalwa, rama, bugawar zuciya da kuma makanta.

Birtaniya ce ta fara amfani da wannan hikimar a duniya

Likitocin cibiyar haihuwa ta birnin Newcastle ne suka samar da wannan hikima, biyo bayan ba su lasisi kan hakan a 2017, kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na BBC.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Jami'an Tsaro Masu Aikata Fashi Da Makami

Ƙasar Birtaniya ce ƙasa ta farko a duniya da ta halasta yin amfani da wannan sabuwar hikima ta MDT a shekarar 2015 bayan shafe lokaci mai tsawo ana gudanar da bincike.

Likitoci sun ce, ba kasafai akan warke daga cututtukan da ke da alaƙa da ƙwayar halittar ta 'mitochondria' ba, kuma cututtukan kan iya janyo asarar rai cikin ƙanƙanin lokaci.

Mutane sun yaba da ci gaban da aka samu

Yara da dama sun rasa rayukansu a dalilin irin cututtukan, wanda da samuwar wannan hikimar ake sa ran za a riƙa haifar yara lafiyayyu.

Masana da ma sauran mutane da dama sun yaba da wannan ci gaba da aka samu wanda ake ganin zai kawo sauyi sosai musamman ga waɗanda ke haihuwar yara da matsalolin cututtukan da ke da alaƙa da ƙwayar halittar ta 'mitochondria'.

Matar da ta haifi yara 44 ta ce ta na son kari

A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wata mata da ta haifi yara 44 ta bayyanawa likitoci cewa tana bukatar karin wasu 'ya 'yan.

Matar 'yar asalin kasar Uganda ta bayyana cewa ba za ta daina haihuwa ba tunda ita ke kula da duka yaran da ta haifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel