“Ina So Mu Yi Gwajin DNA”: Matashi Ya Gano Cewa Diyarsa Na Kama Da Ogan Matarsa

“Ina So Mu Yi Gwajin DNA”: Matashi Ya Gano Cewa Diyarsa Na Kama Da Ogan Matarsa

  • Wani fusataccen dan Najeriya ya nemi a gaggauta yi wa diyarsa gwajin kwayoyin halitta wato DNA domin gano ainahin iyayenta na gaskiya
  • Hakan na zuwa ne bayan mutumin ya ziyarci wajen aikin matarsa sannan ya gano cewa diyarsa na kama da ogan matarsa
  • Mutumin ya ce yana neman asibitin da ke gwajin DNA mai kyau don ya je ayi gwajin sannan ya kore shakku a zuciyarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya ya bukaci ayi gwajin DNA bayan ya gano cewa diyarsa na kama da ogan matarsa sosai.

Rigima ya fara ne bayan mutumin ya ziyarci wajen aikin matarsa sannan ya hadu da oganta a karo na farko.

Miji na so ayi gwajin DNA saboda diyarsa na kama da ogan matarsa
“Ina So Mu Yi Gwajin DNA”: Matashi Ya Gano Cewa Diyarsa Na Kama Da Ogan Matarsa Hoto: Getty Images/ Maskot and Rick Gomez.
Asali: Getty Images

Mutumin wanda ya aika sako zuwa ga wani mai amfani da Twitter @XBrianDennis ya ce yana neman asibitin da ake gwajin DNA mai kyau a Abuja domin ya kore duk wani shakku daga zuciyarsa a lokaci daya.

Kara karanta wannan

“Kana Da Karfin Hali”: Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta a Bidiyo

Dan Najeriya da ke zama a Abuja ya bukaci ayi wa diyarsa gwajin DNA

Mutumin ya ce bayan ya ga ogan matarsa, sai ya gano cewa diyarsa na kama da ogan kamar an tsaga kara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsananin kamar da diyarsa ke yi da ogan matarsa ne yasa yake neman wajen da za a yi mata gwajin kwayar halitta.

Ya rubuta wani sako:

"Na je ofishin matata a ranar Juma'a sannan na ga oganta kamar diyata sak. Ina ta mamakin menene dalilin da yasa diyata bata yi kama da kowa daga cikinmu ba. Matata na so ta haukata ni. Fuskar diyata ba nawa bane."

Masu amfani da Twitter na martani ga labarin inda wasu suka bayar da shawarar wuraren gwajin DNA da mutumin zai ziyarta.

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Wani Mai Bukata Ta Musamman Ya Fashe Da Kuka a Bidiyo Yayin da Matarsa Ta Gwangwaje Shi Da Kyautar Mota

@Inuwaunited ya ce:

"Vignette Hospital Area 11, Garki. Baiya caji da yawa kamar yadda sauran wurare ke yi a Abuja."

@OmobaFash1 ya ce:

"Wahala na zuwa."

@Funmiscute ya yi martani:

"EchoScan wuri ne mai kyau."

Budurwa ta gwara kan samarinta uku a lokaci guda, ta hada su waje daya ba tare da sun sani ba

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata budurwa ta haddasa cece-kuce a Twitter bayan ta bayyana yadda ta yi wa samarinta uku dabara har suka tayata kwashe kayanta zuwa sabon gida ya yadu a soshiyal midiya.

A rubutun wanda @muvatone ta yi a ranar 9 ga watan Yulin 2023,bta yi ikirarin cewa ta fada ma kowanne daga cikin masoyan nata cewa sauran yan uwanta ne daga bangaren mahaifinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel