Hukumar NEMA Ta Yi Gargadin Yawaitar Ambaliya Yayin da Kamaru Ke Shirin Bude Madatsar Ruwa Ta Lagdo
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, kasar Kamaru za ta sako wani ruwan da zai iya jawo ambaliya a Najeriya
- Madatsar ruwan Lagdo ta cika makil, ana son rage adadin ruwan da ke cikinsa don kiyaye faruwa batacciya
- A damina, akan samu yawaitar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, lamarin da ke kisan mutane da yawa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Najeriya - Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta samu sanarwar ankara kan ambaliyar ruwa a gabar kogin Benue.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar nan ne ta fitar da sanarwar a wata wasikar da TheCable ta gani, mai kwanan wata 21 ga watan Agusta.
Wasikar wacce ke dauke da sa hannun Umar Salisu, daraktan ma'aikatar harkokin Afirka ta ce gwamnatin Kamaru na shirin "bude kofofin ruwa na Lagdo Dam da ke kogin Benue nan da kwanaki masu zuwa".
Meye dalilin sako ruwan?
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan ya faru ne saboda mamakon ruwan sama da ya zagaye madatsar ruwan da ke a Arewacin Kamaru.
A cewar Salisu, hukumomin Kamaru za su ke fitar wani karamin adadi ne na ruwan a lokaci guda, kamar yadda rahoto ya bayyana.
A cewarsa:
"Za a yi hakan ne domin ragewa da kaucewa barnar da ruwan zai iya haifarwa a gabar kogin Benue a cikin Kamaru da Najeriya."
Don haka ma’aikatar ta bukaci hukumar ta NEMA da ta dauki matakin dakile yawaitarsa domin rage barnar da ka iya biyo baya.
Martanin NEMA game da ambaliyar uwan
Nonso Ezekiel, mai magana da yawun hukumar NEMA, ya shaidawa TheCable cewa bude kofar madatsar ruwan za a yi shi ne da kadan-kadan.
A cewarsa:
"Muna da cikakkiyar masaniya game da bude madatsar ruwar kuma mun fara daukar matakan kariya ta hanyar wayar da kan al'ummomin da ke kewayen kogin Benue."
NEMA ta bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu tare da bin umarnin hukumar kan yadda za su tsira.
NEMA ta ankarar da mutanen Neja
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta yi kira ga mazauna kananan hukumomi 11 a jihar Neja da su shirya tunkarar matsalar ambaliyar ruwa a watanni masu zuwa, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Shugabar ofishin ayyuuka na Minna, Zainab Sa’idu, ce ta yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa da ta fitar a garin Minna, babban birnin jihar.
Asali: Legit.ng