Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa

Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa

- Akalla mutane 9 suka mutu a kananan hukumomi 9 na jihar Kano, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankunan

- A wani labarin makamancin wannan, mutane 7 suka bakuncin lahira a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa sakamakon iftila'in ambaliya a yankin

- Gwamnatocin jihohin biyu ne suka bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da manema labarai, tare da cewa anyi asarar amfani gona da gidaje

Gwamantin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 9 tare da bayyana mutane 5 da suka samu raunuka a ambaliyar ruwa da ta afku a wasu kananan hukumomi 9 na jihar.

Babban Sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SERERA), Ali Bashir, ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da kamfanin dikllancin labarai na NAN, a ranar laraba.

A kari da hakan, Bashir ya ce waki'ar tra shafi sama da mutane 4,475 a yankunan. Ya bayyana cewa mutane biyar suka mutu a garin Rimin Gado, yayin da wasu uku suka mutu a garin Gabasawa, inda na karshen ya mutu a garin Getso, cikin karamar hukumar Gwarzo.

Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa
Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Malaman makaranta da na kiwon lafiya 2,000 suka mutu a shiyyar Arewa maso Gabas

"A kididdiga, mutane 9 sun rasa rayukansu yayinda mutane 5 suka samu raunuka a wannan iftila'in ambaliyar ruwan wacce ta shafi sama da mutane 4,475," a cewar Bashir.

A cewar jami'in hukumar, har yanzu ana kan tattara bayanai na wasu kananan hukumomi biyar da ambaliyar ruwan ta shafa.

"Muna da kananan hukumomi 14 da ambaliyar ruwan ta shafa, zuwa yanzu mun kammala tattara bayanai akan kananan hukumomi 9 cikin 14," a cewar sa.

Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa
Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa
Asali: Twitter

A wani labarin makamancin wannan:

Shugaban karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa, Abdulrashid Ibrahim, ya ce akalla mutane 7 ne ambaliyar ruwa ta hallaka, tare da lalata sama da gidaje 2000 da gonaki a jihar.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan da ya kai ziyarar jajantawa ga al'umomin da iftila'in ya shafa. Ya bayyana cewa barnar da ambaliyar tayi abin tayar da hankali ne duba da cewa wannan ne karo na farko da aka taba samun irin wannan mummunar ambaliyar tun bayan shekara ta 2003.

Ibrahim wanda ya ce sama da hekta 100 ta gonaki da kuma kayan amfanin gonar mutane akalla 45,000 ambaliyar ta lalata, tare da lalata gidajen su, ya kuma ce ambaliyar ta lalata amfanin gonaki da kiyascin kudin su ya kai miliyoyin naira, da suka hada da Dawa, Gero, Gyada, Alkama, Maiwa da dai sauran kayan hatsi.

KARANTA WANNAN: Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS

Ya bayyana cewa mutanen da suka rasa rayukansu, sun mutu ne a kokarin da suke na barin yankin da ambaliyar ta afku ta hanyar kwale-kwale, cikin hukuncin Allah sai kwale kwalen ya wulkita, inda ya hallaka mutane 7 da ke samansa.

Ya bayyana sunayen garuruwan da ambaliyar ta shafa da suka hada da: Dabi, Auramo, Yakasawa, Algama, Laura, Kayi hawa, Dingare, Siyanku, Nsukum, zangon kanya, Malamawan Yandutse, Kyarama, Sintilmawa , Yan-dutse da kuma Chai-chai Sabuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng