Kowane ‘Dan Majalisa Zai Samu N150m a Rabon N54bn da Za Ayi Domin Yin Ayyuka

Kowane ‘Dan Majalisa Zai Samu N150m a Rabon N54bn da Za Ayi Domin Yin Ayyuka

  • Fiye da Naira biliyan 50 za a batar a majalisar wakilan tarayya domin a aiwatar da kwangiloli a 2023
  • Kowane ‘dan majalisa zai tashi da Naira miliyan 150 da za ayi amfani da ita ayi a bunkasa mazabarsa
  • Daga cikin ayyukan ‘yan majalisar Najeriya akwai yin dokoki, sa ido a gwamnati da gudanar da ayyuka

Abuja - ‘Yan majalisar wakilan tarayya a Najeriya za su samu jimillar Naira biliyan 54 domin su gudanar da ayyukan mazabu a fadin kasar nan.

A rahoton da Punch ta fitar dazu, an ji yadda kowane ‘dan majalisar wakilai zai samu Naira miliyan 150 domin ya kai ayyuka a inda yake wakilta.

‘Yan majalisar da su ka yi magana ba tare da sun bari an kama sunayensu ba, sun tabbatar da doka ta ba su damar kai kwangiloli a mazabunsu.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Ware Miliyan 700 Don Biyawa Daliban Kano Kudin Makaranta a BUK

Majalisar wakilai
Shugaban majalisar wakilai a Najeriya, Tajuddeen Abbas Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Kudin da 'yan majalisa su ke tashi da su

A dokar kasa da tsarin mulki, za a iya ware wani katafaren aiki a mazaba ko shiyyar ‘dan majalisa, wanda zai taba rayuwar wadanda yake wakilta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana warewa Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai wannan kudi a ma’aikatun gwamnatin tarayya bayan irin dawainiyar da ake yi da su.

Haka zalika ‘yan majalisar dokokin da ke jihohi su na samun kudin da za su yi wannan aiki a karkashin kasafin kudin ma’aikatun jihohinsu.

Talakawa su na cikin ha'ula'i

Idan an gama kwangilar, za a samu ya na da dauke da sunan ‘dan majalisar da ya yi sanadiyyar gudanar da aikin, hakan ya bude kofar badakala.

A lokacin da talakawa su ke kuka da tsadar rayuwa, rahoton ya ce gwamnati mai-ci ta kara adadin kudin da ake warewa ‘yan majalisa da N50m a yanzu.

Kara karanta wannan

Tsohon Direba Dan Shekara 72 Ya Shiga Uku, Bayan Lalata Kadarar Miliyan 320 Da Taraktar Da Yake Tukawa

Idan ‘dan majalisa zai samu N150m, babu mamaki kudin da Sanatoci za su samu ya karu sosai a kasar da mata su ke lalata domin su samu na abinci.

Ba yau aka fara wannan aiki ba

A majalisar da Femi Gbajabiamila ya jagoranta tsakanin 2019 da 2023, Honarabul Kwamoti Laori ya tona yadda ake warewa kowane ‘dan majalisa kudi.

Laori mai wakiltar Numan/Demsa/Lamurde ya taba cewa kowanensu ya na samun N100m da zai iya yi wa mutanensa ayyuka a mazabun da yake wakilta.

A wancan lokaci, ‘dan majalisar kasar ya koka da cewa ana samun matsala wajen kasafi, a karshe yake cewa ayyukan da ake yi ba su wuce na N80m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng