Dattijo Dan Shekara 72 Ya Shiga Tasku Kan Lalata Kadarar Miliyan 320 Da Mota a Legas

Dattijo Dan Shekara 72 Ya Shiga Tasku Kan Lalata Kadarar Miliyan 320 Da Mota a Legas

  • An zargi wani direban tarakta mai suna Isiaka Abdullahi da lalata kadarar da ta kai ta miliyan 320 a Ikorodu da ke Legas
  • An ce Abdullahi ya tuka motar taraktar ta sa ne zuwa cikin kasuwar Owode Elede ta Mile 13
  • Sai dai kotu ta bayar da belin Abdullahi kan naira miliyan 5 tare da kawo mutane 2 da zasu tsaya ma sa

Yaba, jihar Legas - An gurfanar da wani dattijo Isiaka Abdullahi, mai shekaru 72 wanda direban tarakta ne, a gaban wata kotun Majistare da ke Yaba a birnin Legas.

An zargi Abdullahi da lalata kadarorin wasu 'yan kasuwa biyu, da darajarsu ta kai ta naira miliyan 320 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An kama dattijo mai shekaru 72 a Legas
An gurfanar da dattijo mai shekaru 72 bisa laifin lalata kadarorin miliyan 320 a Legas. Hoto: Court of Appeal
Asali: UGC

Yadda Abdullahi ya lalata kadarar miliyan 320

Jami'i mai gabatar da ƙara ASP Amedu Adoga, ya ce Abdullahi ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Disamban 2022, lokacin da ya tuƙa motarsa ƙirar tarakta zuwa cikin kasuwa Owode Elede ta Mile 13.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin hakan ne Abdullahi Isiaka da wasu abokan aikinsa suka lalata kadarorin wani ɗan kasuwa da aka ƙiyasta darajarsu a kan naira miliyan 300.

Haka nan duk a cikin wannan lokaci, Abdullahi da abokan aikin na sa sun tattake tarin ayaba da ta kai ta naira miliyan 20, wacce mallakin wani mutumin ce daban.

Mai shari'a Adeola Olatunbosun, ta bayar da belinsa a kan naira miliyan biyar, tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya ma sa.

An kama matashi kan zargin sata a maƙabarta

A baya Legit.ng ta yi wani rahoto kan wani matashi mai kimanin shekaru 28 da aka gurfanar a gaba ƙuliya saboda sata a maƙabarta.

An zarge shi da buɗe ƙaburbura tare da satar wasu ƙarafuna da ake rufe mamata da su da kuɗinsu ya kai naira miliyan ɗaya da ɗigo ɗaya.

Kara karanta wannan

"Badakalar Miliyan 40": Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta

An tuhumi matashin mai suna Mubarak Kajola da laifin keta haddi, sata da kuma mallakar muggan makamai a gaban kotu.

Kotu ta daure wata mata saboda cizon mai sulhu a Abuja

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hukuncin da wata kotu ta yanke kan wata mata da ta kai cizo ga wacce ta zo rabo yayin da suke fada a Abuja.

Kotun ta bukaci wacce ake tuhuma da ta biya kuɗin belin kanta har naira dubu 500 tare da gabatar da wanda zai tsaya ma ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel