Masu Garkuwa Da Mutane Sun Saki Matar Malamin Addini, Sun Kama Wanda Ya Kai Kudin Fansa a Wata Jihar Arewa

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Saki Matar Malamin Addini, Sun Kama Wanda Ya Kai Kudin Fansa a Wata Jihar Arewa

  • Yan bindiga sun sako Misis Bola Ajiboye wacce aka sace a kasuwa tana tsaka da kasuwanci a shagonta
  • Maharan sun sako Ajiboye wacce matar fasto Johnson Olalekan Ajiboye ce, a ranar Laraba
  • Sai dai kuma, sun yi garkuwa da mutumin da ya je kai kudin fansarta kuma sun bukaci a biya naira miliyan 5

Jihar Kwara - Wadanda suka yi garkuwa da Misis Bola Ajiboye, matar Fasto Johnson Ajiboye na cocin RCCG da ke jihar Kwara, sun sako ta.

Sai dai kuma a wani yanayi mai cike da sarkakiya, masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da mutumin da aka aika domin ya kai kudin fansarta, jaridar Vanguard ta rahoto.

Yan bindiga sun yi garkuwa da wanda ya je kai kudin fansa
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Saki Matar Malamin Addini, Sun Kama Wanda Ya Kai Kudin Fansa a Wata Jihar Arewa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yan bindiga sun bukaci miliyan 5 kan wanda ya je biyan kudin fansa

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

Domin su saki wanda suka sace yayin kai kudin fansa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a sake basu naira miliyan 5 kudin fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku tuna cewa an yi garkuwa da Misis Ajiboye ne a shagonta da ke garin Elerinjare a karamar hukumar Ifelodun na jihar Kwara a daren ranar Alhamis na makon da ya gabata lokacin da yan bindiga suka farmaki garin.

An tattaro cewa wadanda suka sace matar malamin addinin sun sakota a ranar Laraba bayan an biya naira miliyan daya a matsayin kudin fansarta tare da kayan abinci da wasu abubuwan da maharan suka bukata.

Wani dattijo a garin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya fada ma manema labarai cewa yan bindigar sun tsare mutumin da ya je kai kudin fansar bayan ya mika masu kudin.

Kara karanta wannan

NYSC: 'Yan Bindiga Sun Nemi Bukata Daya Tak Don Sakin Matashiya 'Yar Bautar Kasa Da Su Ka Sace, Bayanai Sun Fito

Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun kira al'ummar garin sannan sun bukaci a biya su naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa kafin su sako shi.

Dattijon ya ce:

"Muna bakin ciki a garin Elerinjare saboda labarin da ke fitowa daga garinmu. Yanzu mutanenmu na rayuwa cikin tsoro saboda sace-sacen mutane na baya-bayan nan.
"Tafiyar minti 45 ne daga Elerinjare zuwa Ilorin, an gayyaci ni don halartan wani taro a gida kan yadda za mu hada kudi don sakin mutumin wanda ya je kai kudin fansa don sakin matar fasto. Amma ina tsoron yadda zan kai garin.
"Masu garkuwa da shi suna neman al'ummar garin su biya naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa, ta yaya za mu hada wannan kudin yanzu?"

Ya bayyana cewa a yanzu haka an dauki matar faston zuwa wani kebantaccen wuri a garin domin ta samu hutu.

Martanin yan sanda a kan sace wanda ya je kai kudin fansa a Kwara

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi ya bayyana cewa har yanzu ba a sanar da shi komai kan ci gaban ba, rahoton Daily Trust.

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matasa Masu Bautar Ƙasa NYSC

A wani labarin, mun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 8 a kan wata babbar hanya a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Baki ɗaya 'yan bautar ƙasar da lamarin ya shafa suna cikin wata motar Bas AKTC kuma sun fito ne daga Uyo, jihar Akwa Ibom, suka shiga ta Sakkwato a hanyarsu ta zuwa Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel