'Yan Bindiga Sun Harbe Soja 1 Tare Da Sace Buhunan Kudi a Jihar Edo
- Wasu 'yan bindiga ɗauke da makamai sun farmaki wata motar sojoji a jihar Edo
- Mutanen da ake tunanin 'yan fashi ne, sun halaka jami'in soji ɗaya a yayin farmakin
- Haka nan kuma sun yi awon gaba da wasu maƙudan kuɗaɗe da sojojin ke yi wa rakiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Benin City, jihar Edo - Wasu 'yan bindiga da ake tunanin 'yan fashi da makami ne, sun bindige wani soja har lahira a Benin City babban birnin jihar Edo.
Haka nan kuma 'yan bindigar sun yi nasarar ɗauke wasu buhuna da ke dauke da maƙudan kuɗaɗe bayan aikata ɗanyen aikin kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Yadda 'yan bindiga suka harbe soja tare da ɗauke buhunan kudi
Mummunan lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba, a kan titin Akpakpava, daidai shatale-tale na farko yayin da sojojin su uku ke yi wa buhunan da ake kyautata zaton na kuɗi ne rakiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
'Yan bindigar sun zo ne a cikin wata mota ƙirar Toyota samfurin Camry, inda biyu daga cikinsu suka fito daga cikinta sannan suka buɗewa motar da sojojin suke ciki wuta.
Sojojin uku sun yi ƙoƙarin arcewa, sai dai ɗaya daga cikinsu ya yi rashin sa'a, ya fadi ƙasa cikin jini sakamakon harbin da 'yan fashin suka yi ma sa yayin da suka buɗe wuta.
'Yan sanda za su gudanar da bincike kan lamarin
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa 'yan bindigan sun tafi da buhunan kuɗaɗen.
Ya ce wani shaidan gani da ido ne ya bayyanawa 'yan sandan abinda ya faru, inda ya faɗa musu cewa 'yan fashin sun yi awon gaba da wasu jakunkunan 'Ghana-Must-Go' cike da kudi.
Chidi ya ce rundunar 'yan sandan za ta gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin kamar yadda New Telegraph ta wallafa.
'Yan bindiga sun halaka malamin coci a Kaduna
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani malamin coci da wasu 'yan bindiga suka halaka a yayin da ya je gonarsa da ke Kutama a jihar Kaduna.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Kaduna, Joseph Hayab ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kaduna.
Asali: Legit.ng