“Ban Ci Kudinsa Ba", Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta

“Ban Ci Kudinsa Ba", Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta

  • Jarumar Kannywood, Amal Umar ta magantu a kan zargin da ake mata na damfarar kudi da yawansu ya kai miliyan 40
  • Amal ta ce ba gaskiya bane ita bata ci kudin tsohon saurayin nata ba, hasalima maganar aure ce a tsakaninsu
  • Jarumar ta ce ita da kanta ta kai shi kotu ganin girman zargin da ake mata na cewar suna aikata damfara tare

Fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Amal Umar, ta bayyana gaskiyar lamari kan zargin da wani tsohon saurayinta ke mata na cinye masa kudi.

Idan dai za ku tuna, jaruma Amal na fuskantar tuhuma na damfarar wani tsohon saurayinta kudi wanda yawansu ya kai kimanin Naira miliyan 40.

Amal Umar ta ce bata damfari kowa kudi ba
“Ban Ci Kudinsa Ba", Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta Hoto: Amal Umar
Asali: Facebook

Sai a wata hira da abokiyar sana'arta Hadiza Aliyu Gabon ta yi a shirinta mai suna 'Gabon's Room Talk Show' jarumar ta ce sam zargin da ake yi mata ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari’a Ta Bai Wa Magidanci Masauki a Gidan Yari Kan Lakadawa Tsohuwar Matarsa Duka

Maganar aure ta shiga tsakaninmu da shi

Hasalima ta ce sabanin abun da take fadi, ita ce ta kai tsohon saurayin nata kotu saboda girman zargin da yake mata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce shakka babu saurayin ya yi mata alkhairi a lokacin da yake nemanta domin a cewarta har maganar aure ta shiga tsakaninsu domin iyaye sun shiga lamarin.

Sai dai ta ce da tafiya tayi tafiya, sai ta gane yana yi wa mata facakar kudi ta hanyar siya masu manyan motoci, gida, filaye a Kano lamarin da yasa suka rabu. Amma kuma a lokacin da ya shiga matsala sai ta dunga tausaya masa.

A cewarta ya shiga harkar 'crypto ne' inda ta ritsa da shi lamarin da ya kai ga ita ce ta dunga taimaka masa da kudade.

Jarumar ta kuma ce abun ya kai har ta kusa siyar da motarta saboda ta taimake shi amma sai daga baya ta ji wai ana nemanta kan zargin sun aikata damfara tare.

Kara karanta wannan

Kitimurmura Yayin Da Mahaifiya Ta Rikice Bayan Ganin 'Yarta Budurwa A Makale Da Mijinta, Bidiyon Ya Jawo Kace-Nace

Ina ganin kawai ya zabi yin ramuwar gayya a kaina saboda ni yar fim ce

Jarumar fin din ta ci gaba da cewar matashin na so ya huce takaicin kashewa yan mata kudi da ya yi ne amma sai ya zabi yin ramuwar gayya a kansa saboda ita yar fim ce.

Ta ce:

"Kawai daga baya na ji wai ana nema na, me nayi? wai na ci kudi saboda ya san a cikin matan da ya yi mu'amala da su nice ya zo gidanmu ya yi magana da iyayena, ya san komai da komai nawa toh bari ya rama a kaina saboda kuma ina ganin ni yar fim ce, kin san kallon da ake yi wa yan fim daban da sauran matan da suke waje, yana ganin ai ni wurina za a samu kudi. Shine aka zo aka yi wannan abun amma abun da mutane suke tunani ba haka bane.

Kara karanta wannan

Shigar Nuna Tsaraici Da Matar Fitaccen Mawakin Amurka Tayi Ya Fusata Mutanen Italiya, Sun Nemi a Kore Ta

Kan inda magana ta tsaya, jarumar ta ce har yanzu magana na a gaban kotu kuma ance shi ya kai ni kotu, ba shi ya kai ni kotu ba saboda ana tuhumata da abun da ban san da shi ba kuma girman abun kamar ana so a lakaya cewa tare da shi muke yi da shi amma sai aka ce shi ya kai ni."

Ga bidiyon a kasa:

Jaridar Legit.ng Hausa ta aikewa jarumar sako ta shafinta na soshiyal midiya don jin karin bayani daga bakinta amma bata amsa ba.

Ahmed Musa Ya Gwangwaje Jarumi Abdullahi Karkuzu Da Kyautar Gidan N5,500,000

A wani labarin, mun ji cewa shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Super Eagles Ahmed Musa, ya gwangwaje jarumin fim ɗin Kannywood Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu da katafaren gida.

Hakan ya biyo bayan wata hira da shafin Zinariya ya yi da Karkuzu a cikin bidiyo, wacce ta yaɗu sosai a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng