Mahaifiya Ya Rikice Yayin Da Ta Ga Budurwar 'Yarta Makale Da Mijinta, Bidiyon Ya Jawo Kace-Nace

Mahaifiya Ya Rikice Yayin Da Ta Ga Budurwar 'Yarta Makale Da Mijinta, Bidiyon Ya Jawo Kace-Nace

  • Wata mata ta rikirkita intanet bayan ta shiga rudani saboda ganin 'yarta budurwa a makalkale a jikin mijinta
  • A cikin wani faifan bidiyo, an gano matar ta na jawo 'yar tata daga jikin mijin nata inda ta ce ita ya kamata ya daga
  • Mutane da dama sun kushe wannan dabi'a na budurwar inda su ka gargade ta da cewa watarana za ta yi dana sani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani faifan bidiyon da aka gano mahaifi ya dauki 'yar sa budurwa ya girgiza intanet.

Bidiyon wanda @phikex_cruise ta wallafa a Tiktok ta rubuta cewa "mahaifiyata akwai kishi."

Budurwa ta shiga rudani bayan hango 'yarta budurwa a manne da mijinta
Lokacin Da Mahaifiyar Budurwar Ta Ke Kokarin Jawo 'Yar Tata Daga Mijinta. Hoto: @philex_cruise.
Asali: TikTok

A cikin bidiyon an gano budurwar ta makalkale mahaifin nata a rungume, Legit.ng ta tattaro.

Mahaifiyar budurwar ba ta ji dadin haka ba, yayin da ta umarce da ta sauka daga jikin mahaifin nata.

Kara karanta wannan

Wata Bahaushiya Ta Tashi Kan Mutane Da Sigar Rawanta a Wajen Biki, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano mahaifiyar na jawo 'yar tata da karfi kasa inda ta ke cewa ni ya kamata ya daga ba ke ba.

Mutane da dama sun yi martani inda su ke ganin yarinyar ba ta kyauta ba ganin cewa komai na iya faruwa.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun kushe abin da yarinyar ta yi da cewa ba ta kyauta ba.

Precious Baby:

"Idan ba ku kusa da mahaifinku, ku bar wasu irin maganganu a nan, babu komai a ciki."

estelanjiranigabr:

"Ki tambayi kanki, me yasa mahaifiyarki ta ce ki sauko."

Georgina Georgina:

"Ba za ki iya yin haka a Malawi ba, yayin da kika saka kaya haka."

Floxy:

"Yar fari ce, haka kullum muke da mahaifinmu."

William Roland:

"Haba kadan kadan, wannan abu bai yi ba, abin da yafi shi ne ta guji hakan, har yanzu baban ya na da sauran shekaru."

Kara karanta wannan

“Ban Taba Gani Ba”: Jami'ar Soja Mace Ta Dauki Juna Biyu, Ta Baje Kolin Katon Cikinta a Bidiyo

GOLDFISH GLOBAL:

"Wata rana babanki zai baki mamaki."

❤️Faithfaii:

"A al'adar mu haka babban zunubi ne."

Shadow112:

"Watarana zai bayyana ba da dadewa ba."

Bidiyon Kyawawan 'Yan Mata Na Leburanci Ya Girgiza Intanet

A wani labarin, wasu zuka-zukan 'yan mata sun burge mutane yayin da aka gano su su na aikin leburanci don rufa wa kai asiri.

Wasu biyu daga cikinsu na kwaba siminti tare da jidon bulok don kai wata budurwa da take yabe a jikin gini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel