Rashin tsaro: Fafaroma Francis ya ce ayi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya

Rashin tsaro: Fafaroma Francis ya ce ayi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya

- Fafaroma ya na neman a sa mutanen kasar Najeriya a cikin addu’a

- Shugaban Mabiya Katolikar ya yi wannan kira ne jiya ranar Lahadi

- Bayan haka, Malamin Musulunci, Mufti Menk ya yi wa kasa addu’a

Fafaroma Francis ya yi kira ga Duniya ta yi wa Najeriya addu’a. Shugaban addinin ya yi wannan kira ne ganin halin da aka shiga a kasar Afrikar.

Shugaban mabiya darikar Katolika na fadin Duniya, Pontiff, Pope Francis, ya nemi mutane su sa kasar addu’a da ya yi magana a shafin Twitter.

Hakan na zuwa ne bayan zanga-zanar lumuna da aka fara da sunan #EndSARS ya rikide ya canza salo, lamarin ya kai ga ta’adi da barnar dukiyoyi.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya yi amfani da dattaku a lamarin #EndSARS – Sultan

“Mu roki Ubangiji a game da Najeriya, ta yadda za a guje wa duk wani rikici wajen neman zaman lafiya mai daure wa ta hanyar adalci da gaskiya.”

Fafaroma ya rubuta wannan ne a dandalin sada zumunta na Twitter a ranar 25 ga watan Oktoba.

Daga lokacin da Fafaroma ya aika da wannan sako a shafin @Pontifex zuwa yanzu, sama da mutane 17, 000 sun yada sakon a cikin kusan sa’o’i 12.

Mutane fiye da 45,000 su ka nuna sha’awar wannan magana da Dattijon mai shekara 83 ya yi.

KU KARANTA: Hadiman ‘Dan Majalisa su ka yi hayar ‘Yan iska wajen zanga-zangar #EndSARS

Rashin tsaro: Fafaroma Francis ya ce ayi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya
Fafaroma Francis Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Haka zalika a ‘yan kwanakin nan, ta Twitter, Mufti Menk ya sa Najeriya a addu’a, ya roki Ubangiji mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakar tarzoma.

“Ubangiji ka kare kasasu, ka ja ragamar shugabanninta wajen yin daidai. Ka kare Najeriya daga hadari da wadanda ke neman jawo tarzoma da kiyayya.”

A ranar Juma'a kun ji cewa duka Sarakunan kasar Yarbawa sun fusata da kisan masu zanga-zangar #EndSARS da aka yi a Legas a makon da ya wuce.

Da alamu harbe masu zanga-zanga da aka yi a Lekki bai yi wa Manyan Yarbawan dadi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel