Kano Ta Yi Cikar Kwari Saboda Shagalin Bikin Dan Sanata Barau, Matar Kakakin Majalisa Ma Ta Amsa Gayyata

Kano Ta Yi Cikar Kwari Saboda Shagalin Bikin Dan Sanata Barau, Matar Kakakin Majalisa Ma Ta Amsa Gayyata

  • Jihar Kano ta cika ta tumbatsa yayin da ake shagalin bikin dan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin
  • Hajiya Fatima Tajudeen Abbas, matar kakakin majalisar wakilai wacce za ta tsaya matsayin uwar taro a bikin ta isa jihar
  • Tun a ranar Juma'a ne dubban al'umma suka shaida daurin auren Abdullahi Barau da amaryarsa Bilkisu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Garin Kano ya yi cikar kwari yayin da matar kakakin majalisar wakilai, Hon Tajudeen Abbas, Hajiya Fatima Tajudeen Abbas da wasu manyan yan siyasar Najeriya suka isa jihar domin halartan bikin dan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.

An dai daura auren Abdullahi Barau Jibrin da amaryarsa Bilkisu a babban masallacin Juma'a na Isyaka Rabiu da ke Goron Dutse a ranar 19 ga watan Agusta bayan Sallar Juma'a, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sun Yi Kara: Peter Obi, Saraki, Umahi Da Sauransu Sun Halarci Bikin Dan Ekweremadu a Abuja

Hajiya Fatima Abbas
Matar Kakakin Majalisa Da Manyan Yan Siyasa Sun Isa Jihar Kano Gabannin Bikin Dan Sanata Barau Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Adullahi Amir shine angon yayin da amarya Bilkisu ta kasance diya a wajen mataimakin bulaliyar majalisar wakilai, Aliyu Sani Madaki.

Matar kakakin majalisar wakilan ita ce za ta yi uwar taro a wajen shagalin bikin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin manyan yan siyasa da suka halarci daurin auren

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai, Rt Hon Tajudeen Abbas; wasu gwamnonin jihohi, yan majalisa da sauran masu fada aji duk sun hallara a garin.

Da isarta filin jirgin sama na Kano, matar kakakin majalisar ta samu tarba daga Hajiya Aisha Lawal Saji, kwamishinar harkokin mata ta jihar Kano.

Sauran wadanda suka tarbe ta sun hada da Hajiya Sadiya Abdu Bichi, mai ba gwamna shawara ta musamman kan harkokin mata da Bashir Sanata mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin labarai da sauransu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Wike, Umahi Da Sauran Tsoffin Gwamnoni Daga Karbar Fansho

Akpabio ya jinjinawa Peter Obi kan halartan daurin auren dan Barau

A gefe guda, mun ji a baya cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ji daɗin zuwan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi wajen ɗaurin auren ɗan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau.

A ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta aka ɗaura auren ɗan Sanata Barau, Abdullahi Barau da amaryarsa Bilkisu Aliyu Sani Madaki, a masallacin Juma'a na Isyaku Rabiu da ke birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng