Unguwar Zoma Ta Taimakawa Mata Mai Juna Biyu Ta Haihu a Cikin Motar Da Ke Zabga Gudu a Titi, Bidiyon Ya Yadu

Unguwar Zoma Ta Taimakawa Mata Mai Juna Biyu Ta Haihu a Cikin Motar Da Ke Zabga Gudu a Titi, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata unguwar zoma a wani asibitin gunduma a Ghana ta duƙufa aiki domin taimakon wata mata mai ciki ta haihu a cikin motar haya
  • Adams Fatimata ta bayyana wannan abinda ta yi na farko a fannin aikinta a matsayin wanda ta fi jindaɗinsa
  • Bidiyon da ya nuna wani ɓangare na amsar haihuwar a cikin motar da cikakken bayani daga bakin unguwar zoman ya sosa zukatan mutane

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Adams Fatimata, wata unguwar zoma a wani asibitin gunduma a ƙasar Ghana, ta yi ƙoƙari wajen taimakawa wata mata mai juna biyu wacce ke naƙuda ta haihu a cikin wata mota tana cikin tafiya.

Ma'aikaciyar lafiyar wacce ta kwashe shekara bakwai tana aikin unguwar zoma, ta bayyana cewa tana zaune ne a bayan matar lokacin da ta kama naƙuda.

Unguwar zoma ta taimakawa mai juna biyu ta haihu a cikin mota
Unguwar zoman ta yi ta maza ta taimakawa matar ta haihu a cikin mota Hoto: Joynews.com
Asali: UGC

Matar mai juna biyu ta haifi yaro namiji a cikin motar haya

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

A cikin wata hira da JoyNews, Fatimata ta bayyana cewa ta tausayawa matar wanda hakan ya sanya ta taimaka mata ta haifo jaririnta a cikin motar wacce ke tafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Da farko, tsoro na ke ji. Na kwashe shekara bakwai ina aikin unguwar zoma, amma lokacin da na ci karo da lamarinta, na ji tsoro saboda ko kayan aiki irinsu safar hannu bani da ita. Dole sai dai na yi amfani da hannuwana na ciro jaririn, ba zan iya bari ya faɗo a cikin motar ba." A cewarta.

Fatimata ta bayyana yadda ta ke ji dangane da lamarin

Unguwar zoman ta bayyana lamarin a matsayin wanda ta fi jindaɗinsa a shekara bakwai da ta kwashe tana aikin unguwar zoma.

"Abin jindaɗi ne da farin ciki. A cikin shekara bakwai da na yi ina aikin unguwar zoma, yau ita ce ranar farin cikina saboda ina jin cewa na ceto mahaifiya lokacin da ta ke cikin wani mawuyacin hali." A cewarta.

Kara karanta wannan

“Bana Biyan Kudin Haya”: Budurwa Ta Baje Kolin Gidanta Na N250m, Komai Ya Ji a Gidan

Fatimata ta kuma bayyana cewa matar da jaririnta an duba lafiyarsu a asibiti.

Mutane da dama sun kalli bidiyon hirar da aka yi da unguwar zoman wanda tashar JoyNews ta sanya a Youtube.

Kalli bidiyon a nan ƙasa:

Budurwa Ta Koka Bayan An Fasa Aurenta Ana Saura Sati Biyu

A wani labarin kuma, wata budurwa ta shiga cikin damuwa bayan an fasa auren da ta yi shirin yi tare da masoyinta ana saura sati biyu a ɗaura musu aure.

Budurwar ta shiga baƙin ciki kan fasa auren saboda a lokacin tana ɗauke da cikin wata biyar, tace ba za ta yafewa waɗanda suka shiga suka fita aka fasa auren ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel