Yar Najeriya Da Ke Dauke Da Cikin Yan 3 Ta Caccaki Uwar Mijinta Wacce Ta Kira Ta Da Juya

Yar Najeriya Da Ke Dauke Da Cikin Yan 3 Ta Caccaki Uwar Mijinta Wacce Ta Kira Ta Da Juya

  • Wata mata yar Najeriya wacce ke dauke da cikin yan uku ta yi shagube ga uwar mijinta, wacce ta ce ita juya ce
  • A cewar matar wacce ke cike da farin ciki, surukarta ta sha yin hasashen cewa ba za ta taba haihuwa ba
  • A wani bidiyo mai tsuma zuciya, mai cikin ta baje kolin katoton cikinta sannan ta bayyana cewa tana sa ran haihuwa yara fiye da daya

Wata mata mai juna biyu wacce aka bayyana da @valeradabby96 a TikTok ta wallafa wani bidiyo tana mai godiya ga Allah kan cikin yan uku da take dauke da shi.

A bidiyon, an gano matar tana ta rawa cike da farin ciki yayin da ta baje kolin katoton cikinta.

Mace mai juna biyu
Yar Najeriya Dake Dauke Da Cikin Yan Uku Ta Caccaki Uwar Mijinta Wacce Ta Kira Ta Da Juya Hoo: @valeradabby96/TikTok.
Asali: TikTok

Ta bayyana cewa uwar mijinta ta sha nanata cewa ba za ta taba haihuwar da ba a rayuwarta.

Kara karanta wannan

"Ban San Yadda Aka Yi Na Samu Juna Biyu Ba Tare Da Kwanciyar Aure Ba": Matar Aure Ta Gaya Wa Kotu

Matar ta yi wa bidiyon take da sako mai ban sha'awa, na karfafawa sauran mutane gwiwar cewa su yi imani sannan su cafke ni'imarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"In shaa Allah za ku ji kukan yaro a gidanku a shekarar nan. Ku ansa cikin imani," ta rubuta.

Jama'a sun yi martani yayin da mai cikin yan uku ta baje kolin tulunta

Bidiyon ya yadu a soshiyal midiya, inda mutane da dama suka taya matar murna kan juna biyun da take dauke da shi.

Sakon imani na matar ya karfafawa mutane da dama gwiwar ci gaba da neman dacewa.

@eze chinenyenwa Leticia ta ce:

"Na tayaki murna yar'uwa Allah ya yi mun irin yataki."

@Sinachi84:

"Na tayaki murna."

@Ella Bankz ta ce:

"Na tayaki murna Nima na cafke."

@Jullzie ta ce:

"Na tayaki murna Allah yasa a samu kai lafiya."

Kara karanta wannan

“Ya Fi Kudin Jini”: Budurwa Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2, Ta Ce Mahaifiyar Tata Za Ta Fahimce Ta

@faith iheanacho ta yi martani:

" Na tayaki murna ma'ma."

@anekesummer ta ce:

"Amin! Na tayaki murna Allah ya yi mun irin yataki."

@Damexmide13 sta ce:

"Na tayaki murna yar'uwa."

Kalli bidiyon a kasa:

Bayan hade asusun banki suna tara kudi da mijinta, mata ta fece da kudaden

A wani labarin kuma, wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel