An Fasa Auren Budurwa Ana Saura Sati 2 Duk Da Tana Dauke Da Ciki Wata 5

An Fasa Auren Budurwa Ana Saura Sati 2 Duk Da Tana Dauke Da Ciki Wata 5

  • Wata budurwa ta bayyana bakin cikin da ta shiga bayan an fasa aurenta a watan Disamban 2020
  • Budurwar mai suna Aderonke ta ce an fasa auren ne saboda matsala da ta samu da 'yar uwar saurayinta
  • Aderonke ta ce ba za ta taba yafewa matar ba, kamar yadda ta wallafa labarin a TikTok domin tunowa da batun

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ta ba da labarin yadda aka fasa aurenta a watan Disamban 2020.

A wani faifan bidiyo da ta dora a shafinta na TikTok domin tunawa da batun, budurwar mai suna Aderonke ta ce 'yar uwar mijin da za ta aura ce ta sa aka fasa auren.

Budurwa ta koka kan aurenta da aka fasa ana saura sati 2
Budurwa ta ba da labarin yadda aka fasa aurenta ana saura sati biyu. Hoto: @aderonke775
Asali: TikTok

Budurwar ta ce ba za ta taba yafewa 'yar uwar saurayin na ta ba

Aderonke ta ce ba za ta taba yafewa matar ba, wacce ta ce sun samu matsalar da ta janyo sanadi aka fasa auren.

Kara karanta wannan

“Na Zabi Nutsuwa”: Matashiya Da Ta Shafe Shekaru 7 Tan Soyayya Da Namiji Ta Rabu Da Shi Watanni 3 Bayan Sun Yi Aure

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take ba da labarin, Adeoronke ta ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga Disamba, 2020 wanda ya rage saura kwanaki kadan a daura auren na ta.

Adeoronke ta kuma kara da cewa tana dauke da ciki wata biyar a lokacin da aka fasa auren.

A cewarta:

“Na tuna lokacin da aka fasa daurin aurena ana saura sati biyu a yi bikin, saboda ina da matsala da 'yar uwar wanda zan aura, a lokacin ina da ciki wata biyar, na yi kuka na ki ci abinci tsawon kwanaki biyar saboda na ina jin kamar rayuwata ta zo karshe."

Kalli bidiyon da ta dora a shafinta nan kasa:

Martanin da masu amfani da TikTok suka yin kan labarin soke auren ana saura sati 2

Kara karanta wannan

“Ta Ce Ba Za Ta Biya Ni Ba Har Sai Mun Yi Ido Hudu”: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Masoyiyarsa Baturiya a Bidiyo

Wasu daga cikin mabiyan budurwar da ke kafar TikTok sun tofa albarkacin bakunansu dangane da batun, kamar haka:

@Yous_Phinally ta ce:
"Nagode Allah saurayina mai hankali ne, inda ace saurayinki ya tsaya miki, to da babu fashi sai an yi."
@iwattesther ya yi sharhi:
"Ka ga wani abu game da 'yan mata za su nuna kamar an zaluncesu, amma a zahiri suna tafka wata mummunar ta'asa."
@Marto ya ce:
"Wai 'yar uwar saurayinta, yaushe ne wasu mazan za su girma su zama mazajen da za su iya kare matansu."
@damselevelynfunke ta ce:
"Hakan ya faru dani, ina da ciki wata hudu, yanzu dana ya cika shekara 4 kuma an sanya min rana a watan jiya da sabon mijin da zan aura."

Budurwar da ta nuna gidanta na miliyan 250 ta janyo muhawara

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton wata budurwa da ta nuna cikin gidanta na tsabar kudi naira miliyan 250 a kan Intanet da ya janyo muhawara.

Kara karanta wannan

“Uwar Miji Ta Ce Ba Zan Taba Haihuwa Ba”: Yar Najeriya Ta Samu Cikin Yan 3, Ta Nuna Wa Duniya

Wani fitaccen mai watsa shirye-shirye ne ya tambayeta kan ko tana biyan kudin haya, wanda daga nan ne ta ja shi zuwa cikin gidanta don ya ganewa idonsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel