"Cikina Ya Ki Bayyana" Mata Mai Dauke Da Juna Biyun Wata 5 Ta Nuna Shafaffen Cikinta a Bidiyo

"Cikina Ya Ki Bayyana" Mata Mai Dauke Da Juna Biyun Wata 5 Ta Nuna Shafaffen Cikinta a Bidiyo

  • Wata kyakkyawar mata mai ɗauke da cikin wata biyar ta bayar da mamaki a cikin bidiyon TikTok kan yadda cikinta yake ƙarami
  • A yayin da ta sanya bidiyon a shafinta na TikTok, matar mai ɗauke da juna biyu ta nuna shakku cewa ko tana ɗauke da ciki
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyin su kan bidiyon, inda da yawa daga cikinsu suka cewa zai fito a gan shi nan gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mata mai ɗauke da juna biyu mai amfani da sunan @welly.james a TikTok, ta bayar da mamaki bayan ta nuna cikinta ɗan ƙarami wanda bai bayyana ba sannan ta yi iƙirarin cewa juna biyunta ya kai wata biyar.

A cikin bidiyon ta nuna cikinta wanda bai nuna alamun cewa tana ɗauke da jariri a cikinsa ba.

Kara karanta wannan

"Ta Yi Kuskuren Cika Masa Tanki": Rigima Ta Kaure Tsakani Wani Da Dan Najeriya Da Mai Zuba Man Fetur, Bidiyon Ya Yadu

Mata mai juna biyu ta koka
Mata mai juna biyun wata biyar ta koka kan rashin bayyanarsa Hoto
Asali: TikTok

Ta rubuta a ƙasan bidiyon cewa:

"Ina ɗauke da juna biyun wata biyar amma cikina ya tsaya a haka, da wuya idan zai fito ya yi girma."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Welly ta sanya an yi ta muhawara kan junan biyun na ta mai cike da ban al'ajabi, wanda aka bayyana a matsayin kwantaccen ciki.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi sharhi akan bidiyon sun yi tunanin cewa ƙila fa Welly ta samu kwantaccen ciki ne wanda ba ya bayyana.

Martani ƴan soshiyal midiya kan bidiyon

@Princess Kelvin358 ta rubuta:

"Ta ya aka yi kika gano cewa kina da juna biyu idan kwantaccen ciki gare ki. Ta hanyar gwaji ko ta ina?"

@mariodechef0 ta rubuta:

"Zai bayyana lokacin da ya kai watanni takwas."

@mumspride ta rubuta:

"Allah ya taimake ni kada in fuskanci irin haka idan na samu juna biyu, saboda mijina ba zai ba ni shawarma a cikin dare ba."

Kara karanta wannan

"Ki Na Da Kyau Sosai": Tsaleliyar Budurwa Mai Hannu Daya Ta Dauki Hankula Sosai a Yanar Gizo, Bidiyonta Ya Bazu

@Toluwanee ta rubuta:

"Na wa ya bayyana ne a wata na shida, ni da mijina har mun yi faɗa mun gaji, asibiti ne ya raba mana gardama."

@Akpos Ukale ya rubuta:

"Ka da ki damu, ki bari ki kai watanni takwas za ki ga ya girma, matata haka ya kasance da ita har zuwa wajen wata takwas zuwa goma."

Bidiyon Mahaifiyar Wani Katon Matashi Ya Bayyana

A wani labarin kuma, bidiyon wani matashi ya bayyana inda ya nuna mahaifiyarsa wacce ta haife shi.

A cikin bidiyon matashin wanda ƙato ne, ya tsaya yana ta kallon mahaifiyarsa wacce take da ɗan ƙaramin jiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel