Yadda Daliban da Najeriya ta Aika Karatu a Waje Su ke Wahala da Tashin Farashin Dala

Yadda Daliban da Najeriya ta Aika Karatu a Waje Su ke Wahala da Tashin Farashin Dala

  • Gwamnatin tarayya ta saba zaben wasu malaman jami’o’i a Najeriya, ta tura su karo ilmin boko
  • Wadanda ake zaba su na zuwa kasashen ketare ko kuma su zurfafa ilmin zamaninsu a cikin kasar nan
  • Sakamakon tashin da Dalar Amurka ta ke yi, wasu masu karatu a Indiya sun shiga mawuyacin hali

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A karkashin tsarin hukumar TETFund, gwamnatin Najeriya ta kan dauki dawainiyar ‘yan kasar da-dama domin yin karatu a gida da waje.

Legit.ng Hausa ta samu labari daga cikin masu cin moriyar wannan tsari akwai wasu Bayin Allah da ke karatun digirgir a jami’o’in kasar Indiya.

Daliban kasar sun kafa wata kungiya da su ka kira “TETFund Scholars Association in Indiya” a lokacin da Birtaniya ta ke yabawa gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Tashin Dala
Dalibai na kukan tashin Dala
Asali: Original

Wasikar TETFund Scholars Association in Indiya

Labarin da ya zo mana shi ne ‘yan kungiyar ne su ke kukan halin da su ka samu kan su a dalilin canjin tsarin tattalin arziki da aka fito da shi a yau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan TETFund Scholars Association in Indiya sun aika wasika zuwa ga hukumar TETFund da ta turo su domin su san halin da su ke ciki a yanzu.

An aika wasikar ne ta hannun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, kuma Legit.ng Hausa ta fahimci takardar ta isa Abuja a ranar 10 ga Agustan nan.

"Mu na neman karin Dala"

Abin da daliban su ke roko shi ne hukumar taimaka masu da karin Daloli domin su iya rayuwa har su kammala karatunsu da kyau a kasar wajen.

"Ya zama dole mu sanar da ku kalubalen da mu ke fuskanta yanzu a sakamakon karya da kuma yawan hauhawar farashin kaya a Indiya.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

A halin yanzu, farashin Dalar Amurka a CBN ya na tsakanin N750 da N800, matukar bambanci da N450-N460 da aka ba mu kudinmu."

- Kungiyar

Wani hali daliban ke ciki a Indiya?

Wadannan yanayi da aka shiga sun jawo kudin wurin kwana, abinci, zirga-zirga, kiwon lafiya da sha’anin makaranta su ke neman su gagara.

Wasikar ta ce halin tattalin arzikin da daliban su ke ciki ya jawo karatunsu na digiri na biyu (MSC) da na uku (PhD) ya na fuskantar baranza sosai.

Da mu ka zanta da wani a cikin dalibin da ke yin digir-digir ya ce abin da su ke nema daga gwamnati shi ne a ba su damar samun Dala da rahusa.

Hira da wani dalibi mai karatun PhD

"Sun ba mu Dalar Amurka a kan kusan N400, yanzu ana maganar ta kai fiye N900, yanzu mutane su na rayuwa cikin wahala.
Akwai wadanda su ke zaune a wajen makaranta, za a kore su daga gidajensu saboda kudin hayar da za a biya ya nunku sosai.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Ba kowa ba ne za iya biya, a baya da N70, 000 za ka iya samun Rupi N10, 000, amma a yanzu sai ka samu fiye da N10, 000."

- Dalibin Najeriya a Indiya

Dala ta tashi da aka karya Naira

Kwanakin baya aka ji Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin hikimar daidaita farashin kudin waje, aka soke bambanci a kasuwar canji.

Ko da Naira ba za ta tashi ba, wanda mu ka zanta da shi ya ce kyau masu karatu a waje su samu tallafin dala kamar yadda aka rika yi a lokacin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng