Uwar Bari: Shugaban Kasa Tinubu Zai Dawo da Tallafin Man Fetur Daga Yin Wata 2

Uwar Bari: Shugaban Kasa Tinubu Zai Dawo da Tallafin Man Fetur Daga Yin Wata 2

  • Akwai yiwuwar Bola Ahmed Tinubu ya canza shawara game da janye tsarin tallafin man fetur
  • Daga N190 a Mayun, yanzu ana maganar litar fetur zai iya zarce N720 saboda tsarin da aka kawo
  • Babu mamaki gwamnatin tarayya ta sake komawa gidan jiya, a rika kashe kudi domin fetur ya yi sauki

Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na tunanin fito da wani tsarin wucin gadi na tallafin man fetur lura da halin da ake ciki.

A sakamakon yadda farashin gangar mai da kudin kasar waje su ka tashi, The Cable ta ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai iya lashe amansa.

Fadar shugaban kasa ba ta yanke matsaya ba tukuna, amma an bijiro da wannan magana kuma watakila shugaban kasar ya amshi shawarar.

Shugaban Kasa Bola Tinubu
Bola Tinubu ya cire tallafin fetur Hoto:@DOlusegun
Asali: Twitter

Kenya sun dawo da tallafin man fetur

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Wannan rahoto da jaridar ta kadaita da shi ya nuna gwamnatin Najerya za ta iya yin koyi da kasar Kenya wanda ta maido tallafin fetur yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fetur, kananzir da man dizil duk sun tashi a kasar gabashin Afrikan, yanayin da ya yi kama da na Najeriya inda fetur, dizil da gas su ka yi tsada.

A sakamakon wahalar da al’ummar Najeriya su ke ciki tun Mayu a sanadiyyar tsadar man fetur da tashin kudin ketare watakila a koma gidan jiya.

Gwamnati ta na da alkulaman fetur

Ganin a yanzu an san adadin man da ake sha, wata majiya a fadar shugaban kasar ta ce gwamnati ta san nawa ya dace ya tafi wajen biyan tallafin.

Rahoton ya nuna yadda NNPC ya tabbatar da babu shirin da ake yi na ganin fetur ya kara kudi daga N615 a kan lita, ya nuna za a iya karya farashin.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Gwamnati mai-ci ta na ganin an kai matsayin da ba za a rika batar da kudi a kan dillalan mai babu gaira babu dalili ba domin an san dawar garin.

Tsare-tsaren Tinubu su na aiki?

Ana kokarin dawo da tallafin a wani tsari na wucin-gadi ne da za ayi watsi da shi idan abubuwa sun lafa, sannan ana so darajar Dala ta karye.

Tsare-tsaren da Tinubu ya kawo na karya Naira da barin farashin fetur a hannun ‘yan kasuwa bai haifar da ‘da mai ido ba, an shiga matsin lamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng