“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Dan Najeriya Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiya Cike Da Rangwada a Bidiyo

“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Dan Najeriya Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiya Cike Da Rangwada a Bidiyo

  • Wani dan daudun Najeriya mai suna Macmillian ya bayyana dalilin da ya zabi yin shigar mata a rayuwarsa
  • A wani bidiyo da ya yadu, Macmillian ya ce ya zabi wannan hanyar ne saboda ya lura cewa harkar na ja hankalin duniya sosai
  • Dan daudun ya ci gaba da bayyana yadda aka biya shi zunzurutun kudi har naira miliyan 4 don ya yi kamar mace a wani bidiyon waka

Wani dan daudu mai suna @macmillan_makeover a TikTok ya yadu bayan ya wallafa wani bidiyo nasa inda ya fito tamkar mace a ciki.

A cikin bidiyon da ya baza a shafinsa, an gano shi yana tafiyar rangwada yayin da wani mutum ke rera waka tare da binsa a baya.

Namiji yana tafiyar rangwada kamar mace
“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Dan Najeriya Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiya Cike Da Rangwada a Bidiyo Hoto: @macmillianmakeover/TikTok.
Asali: TikTok

Mac ya bayyana cewa an biya shi zunzurutun kudi har dala 5000 (naira miliyan 4) domin ya taka rawar mace a wani bidiyon waka.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

A cewar Mac, ya zabi harkar daudu saboda ta fiye masa domin dai yana jan hankalin jama'a sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Macmillan ya rubuta a bidiyon:

"Pov: Ga ni ina taka rawar mace a bidiyon waka kan 5000$".

Jama'a sun yi martani yayin da namiji ya taka rawar mace kan $5000

Bidiyon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya inda mutane da dama suka cika da mamakin kwarewarsa.

Yayin da mutane da dama suka jinjinawa wannan baiwa tasa, wasu sun caccake shi kan irin harkar da ya zaba ma kansa na yin shigar mata.

@Just-Amaka ta yi martani:

"Ya yi tafiya kan takalma masu tsini fiye da ni da nake mace."

@PRETTY CLAIRE ta ce:

"Fatar jikin gayen nan da yanayin tafiyarsa kan takalma masu tsini ya zarta komai."

@yienong ta yi martani:

"Na so yanayin tafiyar."

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

@Yemi Monday ya ce:

"Tsayin da fatar ne suka dauki hankalina."

@ciellaofficial ta yi martani:

"Gayen nan na sa kaya fiye da ni."

@solomonmichael938 ya ce:

"Allah ya kiyaye, ya aka yi namiji dan uwana yana shiga idona."

Kalli bidiyon a kasa:

Matar aure ta kadu yayin da ta isa wajen bikin mijinta, aminiyarta ce amaryar

A wani labari na daban, mun ji cewa an sha yar dirama a wajen wani shagalin biki lokaci da wata mata ta gano cewa mijinta na auren aminiyarta ne.

Lamarin da aka yada a dandalin soshiyal midiya, ya nuno matar tana fuskantar aminiyar tata cike da radadi a muryarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng