Matashin Dake Shigar Mata Tare da Tsatse Maza Masu son ‘Shan Minti’ Ya Gurfana a Kotu

Matashin Dake Shigar Mata Tare da Tsatse Maza Masu son ‘Shan Minti’ Ya Gurfana a Kotu

  • Wani matashi mai suna Muhammad a jihar Adamawa ya gurfana a gaban kotu kan zargin yin shigar mata tare da damfarar maza masu neman mata
  • Matashin ya sanar da cewa kayan mata yake sakawa su kama hanya da kawayensa inda yake tatse kudaden mazan da ke son kwanciya da shi ko ‘shan minti’
  • Fadi, sunan barikin da Matashin ya dauka, yace kawayensa na bariki ke rufa masa asiri inda yake basu N500 zuwa N1500 daga kudin maza da yake samu

Adamawa - Wani matashi a jihar Adamawa ya bayyana a gaban kotu bayan yin shigar mata domin yaudarar maza tare da tatsar kudi daga hannunsu.

Muhammad Fadi
Matashin Dake Shigar Mata Tare da Tsatse Maza Masu son ‘Shan Minti’ Ya Gurfana a Kotu. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

The Nation ta rahoto cewa, mutumin mai suna Muhammed Abubakar, yace ya saba shiga cikin kayan mata tare da fita da kawaye mata domin samun kudi daga mazan dake neman mata.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Kawayena mata ke rufa min asiri, ‘Dan damfara

Muhammad wanda ke da difloma a fannin kasuwanci daga foliteknik din Adamawa, Yola, yace mata dake rufa masa asiri yana basu N500 su wa N1,500 a kowacce rana a matsayin kason su na damfararsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Muhammad, wanda yace ya sakawa kansa suna Fadi, ya sanar da alkalin kotun majistaren dake Girei inda aka gurfanar da shi cewa, mata dake rufa masa asiri suna sanar da duk namijin da ya nemi ya kwanta da shi cewa yana jinin al’ada ne.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, wannan yaudarar ta Muhammad tazo karshe ne a ranar 16 ga watan Nuwamba a kasuwar Girei inda ya je siyan ‘dan kunne kuma wani mutum da ya zargi katon gardi ne ya gan shi.

Mutumin ya fasa ihu kuma jama’a sun kawo dauki tare da damke shi.

Kara karanta wannan

Gara in Mutu da dai in Gazawa Magoya Bayana, Peter Obi

Kotun da Alkali Martina Gregory ke shugabanta ta umarci a ajiye shi a gidan yari har zuwa 5 ga Disamba.

An kama matashi yayi shigar mata yana rubutawa budurwarsa jarabawa

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa mai kula da jarabawa ya kama wani matashi yana rubutawa budurwarsa jarabawa.

An gano cewa, ya saka gashi doki tare da cakarewa da ado tamkar mace inda ya fente fuskarsa tsaf tamkar budurwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel