Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Zuwa Gungun ‘Yan Ta’adda a Arewacin Najeriya
- Dikko Umaru Radda ya ba jami’an tsaro kwarin gwiwar aukawa wuraren da ‘yan iska ke fakewa
- Wadannan miyagu ne ake zargi su na tare mutane domin karbe masu waya da wasu dukiyoyinsu
- An yi nasarar ram da wasu da ake zargi, Gwamnan Jihar Katsina ya ce a hukunta marasa gaskiya
Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina, ya bada gudumuwa wajen jagorantar jami’an tsaro domin yin ram da wasu miyagu.
Kamar yadda Hadimin Gwamnan ya sanar a dandalin Twitter, Dikko Umaru Radda ya taya ‘yan sanda shiga mafakar ‘yan iska garin Katsina.
Isah Miqdad, mai taimakawa Gwamna a harkokin kafofin sadarwa na zamani ya ce miyagun sun yi suna a kwacen waya da dukiyoyin jama'a.
Za a kawo tsaro a Jihar Katsina
Da wannan samame da aka kai cikin duhun dare, babban mai taimakawa Mai girma Dikko Umaru Radda ya ce ana kokarin ganin bayan ‘yan iskan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun a baya sabon Gwamnan ya sha alwashin tabbatar da tsaro da zaman lafiya jihar ta Katsina, ya ce zai yi amfani da matasa domin ya kawo tsaro.
Miqdad ya kara da cewa an kai harin ne tsakanin karfe 10:00 da 11:30 na dare a cikin birnin. A yanzu 'yan bindiga sun fara neman yadda za ayi sulhu.
Gwamna ya yi mamaya da duhun dare
Kamar yadda za a iya gani a bidiyon da aka wallafa, dare ya tsala lokacin da dakarun ‘yan sanda da Gwamna Radda su ka dura wadannan wurare.
Legit.ng Hausa ta saurari bidiyon, ta ji Gwamnan ya na fadawa jami’an tsaro su yi bincike kan wadanda aka cafke domin hukunta marasa laifi.
Umarnin da Dikko Umaru Radda ya bada shi ne a kyale duk wanda bai da laifi domin ya kama hanyar gabansa, amma a hukunta marasa gaskiya.
Taron da Gwamnan Katsina ya kira
Kafin wannan samame, da safiyar Talatar ne Gwamnan ya kira taron gaggawa da shugabannin jami’an tsaro domin a tattauna halin da ake ciki.
Radda ya ankarar da jami’an tsaron an dawo da aikata laifuffuka iri-iri a wasu bangarorin jihar.
Sanarwar ta ce ganin halin da ake ciki ya batawa Gwamnan rai, ya na mai nuna takaicinsa kan yadda rashin tsaro ya dabaibaye mutanen Jihar.
Dikko Radda ya nada SGS
A farkon makon nan ne aka samu labari jama’ar Jihar Katsina sun ga abin da ba a saba ba da Mataimakin Gwamna ya zama Sakataren gwamnati.
Wasu sun soki nadin amma Hadimin Gwamna Dikko Radda ya fadi hikimar dauko Abdullahi Faskari domin maye gurbin Ahmad Musa Dangiwa.
Asali: Legit.ng