Ba Za Mu Amince Da Tashin Hankali Yayin Zanga-Zanga Ba, IGP Ya Fadawa Kungiyoyin Kwadago

Ba Za Mu Amince Da Tashin Hankali Yayin Zanga-Zanga Ba, IGP Ya Fadawa Kungiyoyin Kwadago

  • Babban Sifetan Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya yi kira ga kungiyar kwadago kan zaman lafiya
  • Egbetokun ya ce akwai hanyoyin sulhu da dama ba tare da an yi zanga-zanga da ka iya kawo cikas a zaman lafiya ba
  • Kungiyar Kwadago, NLC ta shirya gudanar da zanga-zanga don nuna rashin jin dadi kan matakan da gwamnatin kasar ke dauka

FCT, Abuja - Mukaddashin Sifetan Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya nuna damuwarsa kan shirin zanga-zanga da Kungiyar Kwadago ke son yi.

Kungiyar Kwadago ta NLC da ta 'Yan Kasuwa, TUC sun shirya yin zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu kan cire tallafi da kuma sauran matakai ta gwamnati ke dauka.

Egbetokun ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Talata 1 ga watan Agusta a Abuja, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Akpabio Ya Koka Kan Karancin Albashin 'Yan Majalisar Dattawa, Ya Ba Da Dalili

Ya bayyana sauran hanyoyi da za a bi don samun maslaha

Ya ce ya fahimci damuwar NLC amma ya ce akwai hanyoyin da za a bi wurin shawo kan matsalar.

Yayin da ya ke duba 'yancin yin zanga-zangar, Egbetokun ya roki kungiyoyin da su tabbatar sun yi shi cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, cewar Leadership.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce idan ba a yi hankali ba wasu bata gari za su yi amfani da wannan damar wurin tayar da tarzoma tare da lalata shirin su na yin zanga-zangar lumana.

Sifetan ya bukaci kwamishinonin 'yan sanda da sauran manyan jami'an 'yan sanda da su zauna da kungiyoyin don samun daidaito a kan zanga-zangar.

Ya bayyana shirin su na tabbatar da tsaro a kasar

A cikin sanarwar, Egbetokun ya tabbatar da himmtuwar 'yan sandan wurin samar da tsaro da kiyaye rayukan al'umma, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

Ya kara da cewa, rundunar su ba za ta amince da duk wani nau'i na sace-sace ko fashe-fashe ba wasu bata gari za su iya yi yayin zanga-zangar.

Yayin da ake tunanin samun matsalar tsaro a kasar, Egbetokun ya umarci tsaurara tsaro a dukkan bangarorin kasar.

Ya gargadi jami'an 'yan sanda da su saka ido tare da bin doka don tabbatar da samun zaman lafiya.

Sabon IGP Egbetokun Ya Shiga Ganawa Da Manyan Jami'an 'Yan Sanda

A wani labarin, Mukaddashin Sifetan 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya shiga ganawar gaggawa da manyan jami'an 'yan sanda a Abuja.

Rahotanni sun tabbatar cewa taron na gudana ne da manyan jami'an 'yan sanda na kasar a hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Egbetokun ya gargadi 'yan sandan da su hana faruwar laifuka, ba sai abu ya faru a dauki mataki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel