Mutane Na Amfani Da Lambar Mu Don Ciyo Bashi, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gargadi

Mutane Na Amfani Da Lambar Mu Don Ciyo Bashi, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gargadi

  • Jami'an 'yan sanda a birnin Tarayya Abuja sun koka kan yadda ake amfani da lambobin gaggawa na hukumar don cin bashi
  • Rundunar ta ce mutane na amfani da lambobin wurin cin bashin kamfanonin waya daban-daban da sauran laifuka
  • Kwamishinan 'yan sandan birnin, Garba Haruna ya gargadi jama'a akan irin haka inda ya ce za su kama tare da hukunta masu aikata hakan

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan babban birnin Tarayya Abuja ta gargadi 'yan Najeriya kan amfani da lambobinsu na gaggawa don cin bashi.

Kwamishinan 'yan sandan birnin Tarayya, Haruna Garba shi ya bayyana haka a ranar Juma'a 28 ga watan Yuli a Abuja.

'Yan sanda a birnin Abuja sun gargadi jama'a kan amfani da lambar su wurin cin bashi
Rundunar 'Yan Sanda Ta Koka Yadda Mutane Ke Amfani Da Lambar Su Don Ciyo Bashi A Abuja. Hoto: TheNigeriaLawyer.
Asali: Facebook

Kakakin rundunar a birnin, Josephine Adeh a cikin wata sanarwa ta ce kwamishinan ya ba da umarnin kamawa da hukunta masu aikata hakan, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Sadaukar Da Kashi 50 Na Albashinsa Don Hidimtawa Talakawan Kaduna

Ya gargadi jama'a ka amfani da lambar wurin cin bashi

Ya roki jama'a da cewa irin wadannan lambobin gaggawa ba su dace da abin da ake aikatawa da su ba, amfaninsu shi ne kira don taimakon gaggawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar:

"Kwamishinan na gargadin wasu mutane da ke amfani da lambobin don aikata laifuka da batar da jama'a.
"Akwai wasu kuma da ke amfani da lambobin wurin cin bashin kamfanoni ta waya, za mu kama irin wadannan tare da hukunta su dai-dai abin da suka aikata."

Rundunar ta musanta jita-jitar cewa masu garkuwa sun yi amfani da kayansu

Garba ya kuma musanta cewa masu garkuwa sun saka kayan jami'an 'yan sanda don sace mutane 17 a Apo da ke birnin, cewar Leadership.

Ya kara da cewa:

"Kwamishinan 'yan sandan Abuja na tabbatarwa jama'a cewa rahoton da ake yadawa cewa masu garkuwa sun yi amfani da kayan 'yan sanda don sace mutane 17 a Apo ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

"Wannan wasu ne suka kirkira don biyan bukatar kansu, amma babu abin da ya faru makamancin haka a Abuja."

Lauya Ya Kwana A Ofishin ’Yan Sanda Bayan Kama Shi Da Matar Aure A Otal

A wani labarin, wani lauya mai suna Ayo Sogunro ya bayyana iftila'in da ta same shi a wani otal a Abuja.

Ayo ya bayyana cewa ya je aiki Abuja sai wata abokiyar aikinsa ta kawo masa ziyara otal din don magana akan aikinsu.

Ayo ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar 21 ga watan Yuni inda ya ce ya je ne don ganawa akan hakkin dan Adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.