Jami'an NDLEA Sun Halaka Mutum Biyu Yayin da Suka Kai Samame a Jihar Legas

Jami'an NDLEA Sun Halaka Mutum Biyu Yayin da Suka Kai Samame a Jihar Legas

  • An rasa rayukan waɗanda ba ruwansu yayin da jami'an NDLEA suka kai samamen aiki yankin Idi-Oro a jihar Legas
  • Bayanai daga mazauna Anguwar sun nuna cewa da zuwan jami'an suka bude wuta, harsashi ya samu wasu mutu 2
  • An ce dakarun NDLEA ɗin sun kama tulin haramtattun kwayoyi amma sun bar jama'a cikin jimami da alhini

Lagos state - Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kashe mutane biyu a Unguwar Idi-Oro da ke Mushin a jihar Legas.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Channels TV cewa jami’in hukumar sun halaka mutanen ne a wani samame da suka kai yankin Idi Oro a daren ranar Laraba

Jami'an hukumar NDLEA a cikin shirin aiki.
Jami'an NDLEA Sun Halaka Mutum Biyu Yayin da Suka Kai Samame a Jihar Legas Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa jami'an NDLEA sun yi haka ne da nufin kai farmaki maboyar masu ta'amali da miyagun ƙwayoyi a yankin.

Kara karanta wannan

Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina

Majiyar ta bayyana yayin samamen wanda ya dauki tsawon sa’o’i da dama, jami’an sun rika harbe-harbe kan mai uwa da wabi a kokarinsu na cimma burinsu na tarwatsa abin harinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga baya jami’an hukumar ta NDLEA sun bar yankin bayan kama jakunkuna na wasu abubuwa da ake zargin wiwi ce wacce aka fi sani da Indian Hemp.

Yadda jami'an NDLEA suka yi ajalin matasa 2

Majiyar ta ƙara da cewa lokacin da dakarun NDLEA suka dira yankin, matasa sun ƙalubalance su, garin hatsaniyar ne harsasan jami'an suka samu mutum 2, wasu kuma suka jikkata.

Punch ta rahoto cewa wani mazaunin yankin, Olasunkanmi, ya ce nan take waɗanda aka harba suka mutu, kuma mutane ba su ji daɗin rasa rayukan da aka yi ba.

Ya ce harsashin ya samu wani mai suna Yusuf a kansa, yayin da ɗayan wanda har yanzu ba'a gano bayanansa ba, aka harbe shi a ƙirji, duk nan take suka mutu.

Kara karanta wannan

Shari'ar Emefiele: Fayose Ya Ba Tinubu Shawara Kan Matakin Da Ya Kamata Ya Ɗauka a Kan DSS

Duk wani kokarin jin ta bakin mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ci tura domin bai amsa ko ɗaya daga cikin kiran da aka yi masa ba.

Kaduna: Gwamna Malam Uba Sani Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 14

A wani rahoton Gwamna Uba Sani na jihar Ƙaduna ya rantsar da sabbin kwamishinoni 14 a gidan gwamnatinsa ranar Alhamis.

Ya ce a yanzu gwamnatinsa ta ɗauki harama bayan rantsar da mutanen da zasu ja ragamar cika alƙawurran da ya ɗaukar wa al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel