Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7 a Wani Hari a Jihar Bauchi

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7 a Wani Hari a Jihar Bauchi

  • Ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a wasu ƙauyuka dake a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi
  • Gungun ƴan bindigan waɗanda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi sun halaka mutum bakwai a yayin harin da suka kai ƙauyukan
  • Jami'an ƴan sanda da na sojoji sun fita farautar ƴan bindigan da suka tsere bayan sun halaka wasu mutum daga cikinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Ƴan bindiga sun halaka mutum bakwai a ƙauyukan Gara da Gamji cikin gundumar Burra a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Ƴan bindigan waɗanda suka yo gungu sun farmaki ƙauyukan ne inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi, wanda a dalilin hakan suka salwantar da rayukan mutum bakwai da raunata wasu da dama, cewar rahoton The Punch.

Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Bauchi
Yan bindigan sun farmaki wasu kauyukan jihar Bauchi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar harin

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki a Jihar Arewa, Sun Salwantar Da Rayukan Sojoji Da Manoma Masu Yawa

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Wakili ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai ta wayar tarho, rahoton Daily Post ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Yau mun tashi da labarin baƙin ciki. Mun samu kiran gaggawa cewa wasu ƴan bindiga sun farmaki ƙauyukan Gada da Gamji a gundumar Burra cikin ƙaramar hukumar Ningi. Sun yo gungu ne inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi wanda ya halaka mutum bakwai."

Kakakin rundunar ya kuma bayyana cewa jami'an ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji sun fafata da ƴan bindigan inda suka halaka uku daga cikinsu yayin da sauran suka arce ɗauke raunikan bindiga.

"Ɗaya daga cikin jami'an sojojin mutum ɗaya ya samu rauni inda aka garzaya da shi asibiti domin duba lafiyarsa." A cewarsa.

Ya bayyana sunan waɗanda ƴan bindigan suka halaka kamar haka, Ali Usman, Shuaibu Adamu, Yunusa Adamu, Ali Alton, Umar Sabo Ibrahim, dukkaninsu daga ƙauyen Gamji.

Kara karanta wannan

Bayan Farmakar Gidan Atiku, Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Gidan Wani Babban Jigo a Jam'iyyar PDP

Wakili ya kuma ƙara da cewa jami'an ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro da ƴan sakai sun dira cikin dajin domin cafko ƴan bindigan.

'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji a Zamfara

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun salwantar da rayukan sojoji da wasu manoma masu yawa a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai wani mummunan hari ne a ƙaramar hukumar Maru ta jihar inda suka halaka sojoji bakwai da manoma 22.

Asali: Legit.ng

Online view pixel