'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Da Manoma a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Da Manoma a Jihar Zamfara

  • Miyagun ƴan bindiga sun aikata mummunan ɗanyen aiki a jihar Zamfara dakw yankin Arewa maso Yamma ya ƙasar nan
  • Ƴan bindigan dai sun salwantar da rayukan sojoji bakwai da manoma 22 a harin da suka kai cikin wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maru ta jihar
  • Wasu kangararrun shugabannin ƴan bindiga su uku ne dai suka jagoranci kai harin wanda ya janyo asarar rayukan sojojin da manoman

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun halaka jami'an sojoji bakwai da manoma 22 a wata musanyar wuta da aka yi a tsakanin dakarun sojoji da ƴan bindigan a jihar Zamfara.

Fafatawar a tsakanin dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadarin Daji' da ƴan bindigan ta faru ne a kusa da Kangon Garucci na yankin Dangulbi a ƙaramar hukumar Maru ta jihar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Halaka Bayin Allah Masu Yawa a Wani Mummunan Hari a Arewacin Najeriya

Yan bindiga sun halaka sojoji a jihar Zamfara
'Yan bindiga sun halaka sojoji 7 a jihar Zamfara Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Yadda manoman suka rasa ransu

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Sani Baba ya bayyana cewa wasu daga cikin manoman an halaka su ne bayan ƴan bindiga sun ritsa su a gonakinsu yayin da wasu kuma musayar wutar ce ta ritsa da su, rahoton The Guardian ya tabbatar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"A yayin da wasu daga cikin mutanen aka halaka su lokacin suna aiki a gonakinsu, wasu daga cikinsu kuma an ritsa da su a musanyar wutar tsakanin sojoji da ƴan bindigan."
"Ali Kawajo, Damina da wani shugaban ƴan bindiga mai suna 'Black' su ne suka jagoranci kai harin. 'Black' ya bautar da mafi yawa daga cikin manoman yankin inda yake yawan sanya su yin aiki a gonakinsa."

Sojoji sun halaka wasu ƴan bindiga a Zamfara

Kakakin rundunar 'Operation Hadarin Daji', Kyaftin Ibrahim Yahaya, ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Motocin Wani Babban Kwamishina a Najeriya, Bayanai Sun Fito

Haka kuma dakarun sojoji sashi na 1 na 'Operation Hadarin Daji' tare da haɗin gwiwar dakarun sojoji na FOB, sun halaka ƴan bindiga bakwai a ƙauyen Wanke cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar.

Dakarun sojojin sun yi kwanton ɓauna ne akan hanyar da ƴan bindigan su ke bi suna wucewa.

'Yan Bindiga Sun Farmaki Kwamban Motocin Kwamishina

A wani labarin kuma, kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Abia ya sha da kyar a hannun ƴan bindiga a wani mummunan hari da suka kai masa.

Ƴan bindigan sun farmaki kwamban motocin kwamishinan ne lokacin da fita wani rangadi inda suka halaka jami'an ƴan sanda mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel