'Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu Na PDP

'Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu Na PDP

  • Ƴan bindiga sun farmaki gidan tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin
  • A cewar tsohon shugaban na BOT, ƴan bindigan sun farmaki gidan nasa ne wanda yake haya a birnin tarayya Abuja
  • Ya nuna takaicinsa kan yadda ƴan bindigan suka farmaki gidansa da sunan suna neman N5bn da wasu makamai

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Walid Jibrin, ya koka kan yadda ƴan bindiga suka kai farmaki a gidansa da yake haya a birnin tarayya Abuja.

Jibrin ya bayyana cewa ƴan bindigan su takwas sun zo ne cikin manyan motoci ƙirar SUV guda bakwai ɗauke da muggan makamai, cewar rahoton The Punch.

Yan bindiga sun farmaki gidan Sanata Walid Jibrin
'Yan bindigan sun je neman N5bn da wasu takardu a gidan Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun umarci mai kula da gidan mai suna Awwalu da ya kai su ɗakin kwanan shi, inda suka hargitsa shi tare da ɗauke wasu muhimman takardu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Motocin Wani Babban Kwamishina a Najeriya, Bayanai Sun Fito

A cewarsa, sun gayawa mai kula da gidan cewa suna neman N5bn, makamai da wasu takardu sannan daga baya suka lalata masa ɗakin kwanansa kafin su bar gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne dai bayan wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun farmaki gidan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, dake Adamawa.

Abinda ƴan bindigan su ke nema a gidan Sanata Walid Jibrin

Jibrin, ya yin ganawa da manema labarai a Kaduna ranar Talata, ya bayyana cewa akwai sokana wani ya yi tunanin yana da N5bn, inda ya ce 'asusun ajiya ta na banki a fili su ke ga duk hukumar dake son bincikawa'

Ya kuma yi bayanin cewa wannan shi ne karo na biyu da ƴan bindiga su ke farmakar gidansa, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Babbar Kwalejin Ilmi a Najeriya

"Sun ɗauke mai kula da gidan sannan suka ajiye shi a wani waje bayan sun gaya masa cewa suna neman tsabar kuɗi har N5bn da makaman da na ajiye amma basu samu komai ba."ya . II. Nn.6m
"Tuni har na kai rahoton ga Sufetan ƴan sanda na ƙasa wanda ya umarci kwamishinan ƴan sanda na birnin tarayya Abuja, ya kula da lamarin. Kwamishinan yana ci gaba da bincikensa."

An Tsaurara Matakan Tsaro a Gidan Atiku Abubakar

A wani labarin kuma, an ƙara tsaurara matakan tsaro a gidan Atiku Abubakar biyo bayan harin da ƴan Boko Haram suka kai gidansa.

An ƙara tsaurara matakan tsaron ne a gidan Atiku Abubakar wanda yake a birnin Yola, inda aka cafke waɗanda ake zargin ƴan Boko Haram ɗin ne da suka kai hari a gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel