Rabon Tallafin 500bn: Ganduje Ya Caccaki Gwamnatin Jihar Kano Kan Sukar Tinubu

Rabon Tallafin 500bn: Ganduje Ya Caccaki Gwamnatin Jihar Kano Kan Sukar Tinubu

  • Tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci Abba Gida-Gida da ya bi sha'anin mulki sannu a hankali
  • Shawarar Ganduje na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kano ta caccaki shirin tallafin N500bn na rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
  • Tsohon gwamnan ya ce Abba Gida-Gida ya yi saurin sukar shirin sannan ya buƙace shi da ya yi koyi da gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki magajinsa, gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa sukar shirin N500bn na tallafin Shugaba Tinubu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Idan za a tuna dai Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kano ta yi ƙorafi kan rabon tallafin N500bn domin masu ƙananan sana'o'i.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Kwamitin Rabon Kayan Tallafi Na Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Sabbin Bayanai Masu Muhimmanci

Ganduje ya caccaki Abba gida-gida kan sukar Tinubu
Ganduje ya shawarci Abba gida-gida ya bi a sannu Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnan jihar ya ce rabon tallafin ya fifita wasu jihohin akan wasu inda ya yi nuni da jihar Legas za ta samu kaso 47%, yankin Kudu maso Kudu zai samu kaso 17%, yayin da wasu yankunan za su samu kaso ɗan kaɗan, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Sai dai, an buƙaci gwamnatin jihar Kano da jam'iyyar NNPP da su samar da ingantaccen shiri wanda zai rage raɗaɗin da mutanen jihar su ke ciki ba wai su riƙa neman makusa ba a shirin gwamnatin tarayya na rage raɗaɗin tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne dai a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu a yammacin ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli, wacce tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar.

Sanarwar na cewa:

"A maimakon fahimtar yadda tsarin rabon tallafin yake, jihar Kano ta fito fili ta caccaki tsarin kafin daga biyo su fito su janye kalaman da suka yi."

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Yi Magana Kan Tallafin N8,000 Na Shugaba Tinubu, Ya Gayawa 'Yan Najeriya Muhimmin Abu 1 Da Za Su Yi

Ganduje ya buƙaci Abba Gida-Gida ya yi koyi da Uzodimma

Kamar yadda yake ƙunshe a cikin sanarwar, an buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta yi koyi da gwamatin jihar Imo ƙarƙashin jagorancin gwamna Hope Uzodinma, cewar rahoton Vanguard.

A kalamansa:

"A yayin da wasu jihohin suka kafa kwamitocin da za su samar da mafita ta wucin gadi kan lamarin, sannan wasu irin su jihar Imo sun ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N40,000 domin rage raɗaɗin, gwamnatin NNPP a jihar Kano ba ta yi wata huɓɓasa ba."
"A shekarar 2017, lokacin da gwamnatin tarayya ke tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago kan mafi ƙarancin albashi na N30,000, gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samar da mafi ƙarancin albashi na N36,000 inda ya zama ɗaya daga cikin jihohin da suka amince da mafi ƙarancin albashi wanda ya wuce na gwamnatin tarayya."

Ganduje ya ɗora alhakin rashin ƙwarewa da fahimtar abubuwa a matsayin babban dalilin da ya sanya gwamnatin ta ke yin kwan gaba kwan baya da katoɓara wajen fitar da kalamanta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Gwamnan Legas da Wani Gwamnan Arewa a Villa

Gwamnan Kano Ya Musanta Sukar Tinubu

A baya rahoto ya zo cewa gwamnatin jihar Kano, ta yi watsi da rahotannin cewa ta soki gwamnatin Shugaba Tinubu kan rabon tallafin N500bn.

Gwamnatin ta bayyaan cewa ko kaɗan ba a fahimci kalamanta ba kan tsarin rabon tallafin na N500bn domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel