Bayan Dogon Cece-Kuce, Davido Ya Yi Martani Kan Shirmammen Bidiyon da Ya Yada Na Izgili Ga Sallah

Bayan Dogon Cece-Kuce, Davido Ya Yi Martani Kan Shirmammen Bidiyon da Ya Yada Na Izgili Ga Sallah

  • Shahararriyar mawakin Najeriya Davido na ta yawo a yanar gizo a 'yan kwanakin nan saboda faifan bidiyon waka na sabon yaronsa Logo Olori da ya yada
  • Al’ummar Musulmai da malamansu sun yi kira ga Davido, inda suka zargi mawakin da muzanta addinin Musulunci kan abin da ke zayyane a faifan bidiyon
  • Davido dai bai yi gaggawar mayar da martani ga yadda ya tunzura al'ummar Musulmi ba, a karshe yanzu kuma ya mayar da martani, kuma batunsa bai dace ba

Fitaccen mawakin Afrobeat, Davido ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta a karshen makon nan tun bayan da ya saki wani faifan bidiyon wani yaronsa na waka, inda ake yin wasa da kuma izgili ga sallah.

Hadimin tsohon shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya soki mawakin, inda ya ce faifan bidiyon wakar na nuna izgili ga abin Musulunci yafi mutuntawa wato sallah.

Kara karanta wannan

Ba ma wasa da Sallah: Ali Nuhu ya yiwa Davido kalamai masu zafi kan bidiyon bata Sallah

Bashir da sauran Musulmi masu da ma malamai basu ji dadin abin ba, inda suka bukaci Davido ya sauke wannan faifan bidiyo, tare da nuna nadama da muzanta addininsu.

Yadda Davido ya sake tunzura al'ummar Musulmai
Davido ya tunzura Musulmai a Najeriya da ma duniya | Hoto: @davido/@bashirahmad
Asali: Instagram

"Za su ji a jikinsu" - Davido ya mayar da martani ga kiran da ake masa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga karshe dai Davido ya yi magana, sannan ya amsa kiran da Musulmai ke masa da kalamai masu kama da raini da barkwanci a shafin Twitter.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su nuna masa ainihin laifinsa na yada faifan bidiyon wakar da ba tasa ba.

Daga nan Davido ya yaba wa sabon yaron nasa, Logos Olori, yana mai cewa, "Za su ji a jikinsu."

Martanin jama’a bayan bayanain Davido

A kasan rubutunsa, mutane da yawa sun yi martani, ga kadan daga abin da suke cewa:

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Tallafin Fetur Ta Bugi Gwamnoni, Ana Tunanin Rage Facakar Kudi

@Inno4Chi:

"Ni ne CIA. Bayan cikakken bincike da duba ga bidiyon ka, mun alanta cewa ya dace kuma ya daidai a watsa shi a duk dandamali na talabijin na yanar gizo da na duniya."

@abazwhyllzz:

"OBO ka danna wuyansu fa. Ina goyan bayan ka, babu wanda ya isa ya yi wani abu."

@YoungestDraiyz:

"Ka bari su share maka hanya."

@Lankystillfancy:

"Su koyaushe suna ji a jikinsu ai."

@real_PKC:

"Za su yi bayani har su gaji, babu shaida."

@yazeed_sabo:

"Allah ya shiryar da kai batacce ne, ni masoyinka ne tun ina karami amma ba zan iya kallonka kana raina addinina ba, tabbas ka rasa mutum daya cikin masoyanka!"

@Ishencello:

"Kana neman magana ne kawai ."

@Abdallahmisilli:

"Bayan korafi da gyara da aka yi masa, wannan mutumin ya ki daukar mataki kan wannan bidiyon. Sakacin da ya yi da gangan na barin bidiyon ya ci gaba da zama a kan shafinsa duk da korafin da ake yi na nuna halinsa na rashin mutunta al'ummar Musulmi."

Kara karanta wannan

Kaico: Davido ya saki wata wakar da ta ke izgilanci ga Sallah, ya sha caccaka daga Bashir Ahmad

@YakubuNe:

"Wannan ba daidai ba ne, ba za mu iya dauka ba."

Ali Nuhu ya yiwa Davido wankin babban bargo

A gefe guda, Musulmai a Najeriya na ci gaba da bayyana fushi da wani bidiyon da mawaki Davido ya yada a kafar sada zumunta na wani yaronsa.

A jiya Asabar ne kafar Twitter ta dauki dumi bayan da aka ga bidiyon da ke izgila da ibadar Muslmi; sallah a yayin da katti ke tika rawa.

A martanin da ya yi, Ali Nuhu, fitaccen dan wasan kwaikwayon Kannywood ya yi Allah wadai da abin da mawakin ya yi na muzanta ibadar Musulma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel