Ali Nuhu da Sauran ’Yan Najeriya Sun Yiwa Davido Wankin Babbar Bargo Kan Bidiyon da Ya Yada

Ali Nuhu da Sauran ’Yan Najeriya Sun Yiwa Davido Wankin Babbar Bargo Kan Bidiyon da Ya Yada

  • Ali Nuhu ya shiga sahun wadanda suka yiwa Davido kaca-kaca a kafar sada zumunta kan yada wani bidiyon waka da ya muzanta sallah
  • An ga wnai bidiyon da yaron Davido ya yi na yadda ake sallah da kuma yadda aka barke da rawa bayan idar da sallar
  • A baya, hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi Allah wadai da bidiyon, inda yace ya kamata mawakin ya fito ya ba Musulmai hakuri

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Musulmai a Najeriya na ci gaba da bayyana fushi da wani bidiyon da mawaki Davido ya yada a kafar sada zumunta na wani yaronsa.

A jiya Asabar ne kafar Twitter ta dauki dumi bayan da aka ga bidiyon da ke izgila da ibadar Muslmi; sallah a yayin da katti ke tika rawa.

A martanin da ya yi, Ali Nuhu, fitaccen dan wasan kwaikwayon Kannywood ya yi Allah wadai da abin da mawakin ya yi na muzanta ibadar Musulma.

Kara karanta wannan

Kaico: Davido ya saki wata wakar da ta ke izgilanci ga Sallah, ya sha caccaka daga Bashir Ahmad

Ali Nuhu ya caccaki Davido
Hotunan Ali Nuhu da mawaki Davido | Hoto: @realalinuhu, @davido
Asali: Instagram

Kana ya bukace shi da ya gaggauta janyewa da kuma cire bidiyon a kafar sada zumunta tare da ba Musulmai hakuri kan abin da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ali Nuhu:

“Na ci karo da faifan bidiyo mai cike sarkakiya da @davido ya yada, duk yadda muke son zama masu fikira a fagagenmu daban-daban ya kamata mu koyi mutunta addini, al'adu da tsarin wasu.
“Wannan ba abin yarda ba ne kwata-kwata a Musulunci. Ya kamata ka cire wannan bidiyon kuma ka ba da hakuri kan muzanta al'ummar musulmi baki daya.”

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Baya ga batun Ali Nuhu, mutane da yawa sun yi martani kan wannan lamari, Legit.ng Hausa ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa kamar haka:

@a.u_autos:

“Davido yana ganin ya fi mabiyansa ne, ba tare da sanin cewa shi ba komai bane idan ba mabiyansa ba.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Bidiyon Yadda Amarya Ta Kama Wasa Da Angonta a Wajen Budar Kansu Ya Dauka Hankali

“Faduwarsa ta fara kenan.”

@fabulous_nosh_recipes:

“Ya kamata ya mutunta addininmu ya sauke wancan bidiyon.”

@Ahmerd_natasidi:

“Na yi nadama da na taba kiran kaina mai son Davido, mu musulmai muna daraja addininmu akan komai, ko dai ka sauke wannan shirmen da kuka saka ko kuma mu ci gaba da tsine muku har karshen rayuwarmu.”

@Sarki_sultan:

“Mu Musulmi ba za mu taba yarda da irin wannan rashin mutunci, Musulunci ya koyar da mu yadda ake mutunta addinin juna.
“Ko dai Davido ya fito ya ba da hakuri ko kuma a nan Arewa za mu kasance muna jiran ya tako kafarsa yankin.”

@jarmari01:

“Manta kai selebiriti ne, addininmu yana sama da kai. Muna son addininmu fiye da kanmu.
“To ta yaya kake ganin za ka muzanta addininmu, ka yi tunanin za mu yi shiru haka?
“Wancan shirmammen bidiyonku na ya ci mutuncin addininmu kuma mu Musulmi ba za mu yarda ba......”

A tun farko, Bashir Ahmad ya bayyana rashin jin dadi da ganin bidiyon da mawakin ya yada a kafar Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel