Ya Kamata Yan Najeriya Su Mara Wa Tinubu Baya, Zai Zuba Aiki, Oba Na Benin

Ya Kamata Yan Najeriya Su Mara Wa Tinubu Baya, Zai Zuba Aiki, Oba Na Benin

  • Basaraken Benin a jihar Edo, mai martaba Ewuare II ya ziyarci shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
  • Bayan ganawarsu, Sarkin ya buƙaci yan Najeriya su goya wa Bola Tinubu baya domin zai zuba musu ayyukan alheri
  • Ya ce shi da sauran sarakunan gargajiya zasu mara wa shugaban kasa baya domin abinda yake buƙata kenan a yanzu

FCT Abuja - Oba na Benin a jihar Edo, Mai martaba Oba N’Edo Uku’Akpolokpol, Ewuare II, ya yi kira ga 'yan Najeriya su mara wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya.

Fitaccen Sarkin ya bayyana cewa a halin yanzu ba bu abinda shugaban ƙasar ya fi buƙata kamar goyon bayan mutanen da yake jagoranta, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Oba na Benin tare da shugaban ƙasa Tinubu a Villa.
Ya Kamata Yan Najeriya Su Mara Wa Tinubu Baya, Zai Zuba Aiki, Oba Na Benin Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Basarken ya yi wannan furuci ne yayin zantawa da yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan gana wa da shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Gwamnan Legas da Wani Gwamnan Arewa a Villa

Sarkin ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu zata yi aikin da ya dace a zamanin mulkinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kamata yan Najeriya su goyi bayan shugaban ƙasa, zai zuba aiki a ƙasar nan, alamu sun nuna ya shirya tsaf. Ya fara tun daga ranar farko kuma kowa ya gani, don haka ya kamata a mara masa baya."
"Tabbas zan goyi bayan Tinubu kuma sauran sarakuna zasu goya masa baya, ya zama wajibi mu taimaka wa shugaban ƙasa ya samu nasara."

- Oba na Benin.

Menene dalilin ziyarar da Oba ya kai wa Tinubu?

Sai dai har kawo yanzu ba a bayyana asalin dalin wannan ziyara da Oba ya kai wa shugaban ƙasa har Villa ba ranar Jumu'a, kamar yadda rahoton Vanguard ya tabbatar.

Amma ana hasahen cewa mai yuwuwa ya je ne domin taya Tinubu murnar rantaar da shi a matsayin shugaban ƙasa da kuma tattauna wasu batutuwa da suka shafi 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Babban Sarki da Tawagarsa a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

CJN: Ɗan Shugaban Alkalan Najeriya Ya Bi Sahun Mahaifinsa, Ya Samu Babban Muƙami

A wani rahoton kun ji cewa Ɗan babban Alkalin Alkalan Najeriya ya bi sahun mahaifinsa, ya zama Alƙalin babbar Kotun tarayya.

Hukumar shari'a ta ƙasa (NJC) ta naɗa ɗan shugaban alkalan Najeriya, Mai shari'a Olukayoode Ariwoola, a matsayin alkalin babbar Kotun tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel