Kotu Ta Kori Ƙarar da Hukumar EFCC Ta Shigar da Rochas Okorocha

Kotu Ta Kori Ƙarar da Hukumar EFCC Ta Shigar da Rochas Okorocha

  • Babbar Kotun Abuja ta kori ƙarar da aka shigar da tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha
  • Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ya maka Okorocha gaban kotun bisa zargin satar kuɗin talakawa
  • Alkalin Kotun ya ce ƙarar cin mutuncin shari'a ne saboda EFCC ta shigar da irinta gaban babbar Kotuɓ tarayya kuma ta yanke hukunci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Babbar Kotun birnin tarayya Abuja ta yi fatali da ƙarar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta shigar da tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

Punch ta ce Alkalin Kotun, mai shari'a Yusuf Halilu ne ya kori ƙarar yayin yanke hukunci kan ƙarar da EFCC ke tuhumar tsohon gwamnan da almundahana da cin mutuncin Ofis.

Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha.
Kotu Ta Kori Ƙarar da Hukumar EFCC Ta Shigar da Rochas Okorocha Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Alkalin Kotun ya ce tuhumar da EFCC ke yi wa Sanata Okorocha raina shari'a ne saboda hukumar ta shigar da makamanciyar wannan kara kan wanda ake zargi a babbar Kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jiga-Jigai a Villa, Ya Faɗi Yadda Ya Zama Shugaban ECOWAS

Bisa haka Kotun ta kori ƙarar nan take bisa hujjar cewa babbar kotun tarayya ta riga ta wanke tsohon gwamnan daga zargin da EFCC ta shafa masa a watan Disamba, 2022.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda jami'an EFCC suka kama Okorocha

Idan baku manta ba a watan Mayun shekarar da ta gabata, jami'an hukumar EFCC suka mamaye gidan Sanata Okorocha da ke Maitama a babban birnin tarayya Abuja kuma suka kama shi.

Hukumar ta yi zargin cewa Okorocha ya yi fatali da, "Dukkan gayyatar da ta aika masa bayan ya tsallake sharaɗin belin da ta ba shi tun da farko."

Amma a ɓangarensa, Okorocha, wanda ya shiga tseren neman tikitin shugaban ƙasa a inuwar APC, ya zargi EFCC da garkuwa da shi a cikin gidansa ba gaira ba dalili.

Menene asalin zargin da EFCC take wa Okorocha?

Kara karanta wannan

Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

A ranar 24 ga watan Janairu, 2022, EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 17 da take wa tsohon gwamnan waɗanda suka shafi wawure kuɗin talakawa da kadarori da suka kai biliyan N2.9.

Hukumar na zargin Okorocha da aikata laifukan a tsakanin 2011 zuwa 2019 lokacin da yake kan kujerar gwamnan Imo, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Abinci a Najeriya, Uche Nwosu

Rahoto ya nuna cewa An bayyana ainihin dalilan da ya sanya shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan samar da isasshen abinci a Najeriya.

Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati ya ce dokar ta nuna Tinubu na da fahimta kuma yana bibiyar halin da 'yan ƙasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel