Ban Yi Tsammanin Zama Shugaban ECOWAS Ba, Shugaba Bola Tinubu

Ban Yi Tsammanin Zama Shugaban ECOWAS Ba, Shugaba Bola Tinubu

  • Shugaba Tinubu ya ce bai taɓa tunanin za'a zabe shi a matsayin shugaban ECOWAS a taron farko da ya halarta ba
  • Ya ce ya zama wajibi a ƙasashen Afirka su gina Demokuraɗiyya mai ɗorewa matuƙar suna buƙatar samun ci gaba
  • Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisa zata ci gaba da nara wa Tinubu baya domin sauke nauyin da ke kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai taɓa tsammanin mambobin ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS zasu zaɓe shi a matsayin shugaba ba.

Sai dai duk da haka shugaban ƙasar ya ce zaɓen da aka masa kira ne na aiki wanda ke bukatar zage dantse da aiki tuƙuru, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban Tinubu da tawagar shugabannin majalisar dattawa.
Ban Yi Tsammanin Zama Shugaban ECIWAS Ba, Shugaba Bola Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis sa'ilin da ya karɓi bakuncin jagororin majalisar dattawa karkashin jagorancin shugabansu, Sanata Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

Dalla-Dalla: Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya

Sanatocin sun kai ziyara fadar shugaban ƙasa ne domin taya shugaba Tinubu murnar zama sabon shugaban ƙungiyar ECOWAS.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da zai sa mu samu ci gaba a Afirka - Tinubu

Da yake jawabin, Tinubu ya ce matuƙar ana son Najeriya da sauran kasashen Afurka su samu ci gaba wajibi a rungumi tsarin demokuraɗiyya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake ya fitar ranar Alhamis, Bola Tinubu ya ce:

"Tilas Demokuraɗiyya ta tsira, muna buƙatar haka domin mu sami ci gaba. Ya kamata mu tura alama mai kyau ga sauran ƙasahen duniya cewa mun shirya kasuwanci."

Shugaban Tinubu ya yi alkawarin cewa ba zai bar 'yan Najeriya su ji kunya a wajen kokarin sauke nauyin da Allah ya ɗora masa duk da kalubalen da ake fuskanta ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Batun Samar da Abinci a Najeriya, Ya Bada Sabon Umarni

Ko me yasa aka zabi Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS?

Tun a farko, shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio ya ce zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS a taron farko da ya fara halarta ya nuna yardar da sauran takwarorinsa na ƙasashen Afirka suka masa.

Ya ce majalisun tarayya zasu ci gaba da mara wa shugaban baya domin sauke haƙƙin da ke kansa da kuma cika burin inganta Najeriya, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya

A wani rahoton na daban kuma Masana sun bayyana yadda dokar ta ɓaci zata taka rawa wajen daidaita rayuwar 'yan Najeriya masu matsakaicin ƙarfi.

A cewarsu, dokar ta ƙara bayyana alamun cewa shugaban ƙasa Tinubu yana sauraron koken talakawan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel