Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Abinci a Najeriya, Uche Nwosu

Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Abinci a Najeriya, Uche Nwosu

  • An bayyana ainihin dalilan da ya sanya shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan samar da isasshen abinci a Najeriya
  • Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati ya ce dokar ta nuna Tinubu na da fahimta kuma yana bibiyar halin da 'yan ƙasa ke ciki
  • A cewarsa, shugaban ƙasa ya ɗauki wannan matakin ne domin magance raɗadin cire tallafin man fetur

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Imo, Uche Nwosu, ya faɗi muhimmin dalilin da ya sa shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan samar da abinci.

Nwosu ya ce shugaban ƙasa ya sanya wannan dokar ta ɓaci ne domin daƙile wahalhalun da suka biyo bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Shugaba Tinubu tare da Uche Nwosu.
Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Abinci a Najeriya, Uche Nwosu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ɗan siyasan ya yaba wa shugaban Tinubu bisa wannan mataki da ya ɗauka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jiga-Jigai a Villa, Ya Faɗi Yadda Ya Zama Shugaban ECOWAS

Sanarwan ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Babu tantama muna maraba da matakin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na ayyana dokar ta ɓaci kan samar da isasshen abinci, daidaita farashi da ɗorewa, wannan ci gaba ne da muke fata."
"Bisa wannan mataki, shugaban kasa ya nuna cewa shi mutum ne mai fahimta kuma ya san wahalar da tuge tallafin man fetur ya jefa yan Najeriya, musamman tattalin arzikin magidanta."
"Halin da muka tsinci kanmu a ƙasar nan na tashin farashin kayan abinci babban abin damuwa ne, amma alamu sun nuna wannan gwamnatin zata yi hanzarin lalubo hanyoyin warware ƙuncin rayuwar da talakawa suka shiga."

Mista Nwosu ya ƙara da cewa yadda Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a samar da abinci, alama ce dake nuna mutum ne mai bibiyar halin da yan ƙasa suke ciki.

"Bugu da ƙari ya nuna cewa shi ba shugaba bane da zai kauda kai kan tashin farashin kayan abinci da kuma yadda hakan ke shafar mutanen Najeriya."

Kara karanta wannan

Dalla-Dalla: Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya

Ban Yi Tsammanin Zama Shugaban ECOWAS Ba, Shugaba Bola Tinubu

A wani labarin na daban Shugaba Tinubu ya ce bai taɓa tunanin za'a zabe shi a matsayin shugaban ECOWAS a taron farko da ya halarta ba

Sai dai duk da haka shugaban ƙasar ya ce zaɓen da aka masa kira ne na aiki wanda ke bukatar zage dantse da aiki tuƙuru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel