“Aure Ni”: Baturiya Za Ta Ba Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

“Aure Ni”: Baturiya Za Ta Ba Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

  • Wata baturiya ta nuna kudirinta na son yin aure sannan ta sanya garabasa ga maza domin kada damar ta kufce masu
  • Matashiyar wacce ke zaune a kasar Birtaniya, ta yi alkawarin baiwa duk mutumin da ya zama mijinta kyautar biza
  • Maza da dama sun cika sashin sharhin rubutun nata inda suka nuna ra'ayinsu na son zama mijinta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar baturiya wacce ke neman mijin aure ta yi alkawarin bayar da kyautar biza ga duk namijin da ke son zama mijinta.

Wani dandalin kulla soyayya na TikTok, ya wallafa dan gajeren bidiyo na matar da ba a bayyana sunanta ba da garabasar kyautar biza da za ta bayar.

Budurwa na neman mijin aure
“Aure Ni”: Baturiya Za Ta Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta Hoto: @holly_matrimony
Asali: TikTok

Kamar yadda shafin ya rahoto, matar wacce ba a bayyana sunanta ba tana son shiga daga ciki kuma tana zaune ne a kasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

“Sharadi Ba Za Ka Yi Mun Kishiya Ba”: Budurwa Ta Yi Alkawarin Baiwa Duk Wanda Ya Aureta Gida, Mota da Miliyan 50 a Bidiyo

Mazaje daga kashe daban-daban sun nuna ra'ayinsu na son ganin sun yi nasara yayin da suka yi martani ga bidiyon da ya yadu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

macanoow28 ya ce:

"Kwarai idan kin shirya muna iya auren junanmu yanzu haka ina kasar Kenya wuri mafi kyau a duniya."

Sam Ochiti ya ce:

"Ya dai zuma gani nan ina jiranki yarinya don Allah."

SK ya ce:

"Ya dai ina da ra'ayi.
"Daga wacce kasa kike.
"Ina kasar Indiya."

Saeed Shah Mohmmad ya ce:

"Ina ra'ayi kuma ina sonki shin kina sona kema?"

Bawanaa Yaw ya ce:

"Ina kwana kawata don Allah zan iya zama abokinki."

peace ta ce:

"Haka kike fadi tuntuni don tara kwamet, don Allah ki ci gaba da zama babu miji har tsawon rayuwarki."

sudi ya ce:

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Maimaita Tufafin Da Mataifiyarta Ta Sanya Shekaru 29 Da Suka Gabata a Ranar Aurenta

"Ni dogo ne baki daga kasar Kenya don Allah zo ki daukeni na gaji da nan."

Zan ba da gida, mota da miliyan 50 ga duk wanda ya aureni, budurwa

A wani labari makamancin wannan, wata kyakkyawar budurwa yar arewa ta sha alwashin bayar da gida, mota da kudi har naira miliyan 50 ga duk namijin da ya yi nasarar aurenta.

Matashiyar wacce ta bukaci maza su shiga gasar ta ce sharadinta shine duk wanda ya yi nasarar mallakarta a matsayin matarsa ba zai yi mata kishiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel