“Ba Zan Karbi Kudin Hayarki Ba”: Budurwa Ta Shiga Dimuwa Yayin da Mai Gidansu Ke Nemanta

“Ba Zan Karbi Kudin Hayarki Ba”: Budurwa Ta Shiga Dimuwa Yayin da Mai Gidansu Ke Nemanta

  • Wata budurwa yar Najeriya ta nemi shawarar jama'a kan yadda za ta fitar kanta daga tsaka mai wuya
  • A cewarta, mai gidan da take haya ya gabatar mata da wata bukata mai ban mamaki kuma ta shiga dimuwa kan ta amsa tayinsa ko a'a
  • A wata wallafa da ta yi, ta bayyana muradin mai gidansu na son kulla alaka da ita a madadin kudin hayarta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mai amfani da Twitter mai suna @Gabri3llaa ta bayyanawa jama'a halin da take ciki bayan mai gidansu ya gabatar mata da wata bukata mai ban mamaki.

A cikin wata wallafa da ta yi a shafinta, ta bayyana cewa mai gidansu ya nemi su yi ban gishiri na baki manda a tsakaninsu wato ya nemi su kulla alaka sai ya yafe mata kudin haya idan ta yarda.

Kara karanta wannan

'Na Gaji Da Dawainiya': Matar Aure Ta Nemi Saki Bayan Daukar Nauyin Mijinta Shekaru 10

Matashiya ta ce mai gidan da take haya yana nemanta
“Ba Zan Karbi Kudin Hayarki Ba”: Budurwa Ta Shiga Dimuwa Yayin da Mai Gidansu Ke Nemanta Hoto: Bloomberg/Getty images, Gabri3lla/Twitter
Asali: UGC

Kalamanta:

"Mai gidan da nake haya yana so ya kulla alaka da ni a madadin kudin hayata. Na shiga rudani sosai kan abun da zan yi. Akwai shawara?"

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rubutun nata ya haddasa cece-kuce daga wajen jama'a inda mutane da dama suka yi Allah wadai da abun da mai gidan ya yi sannan sun nuna goyon bayansu ga matar.

Martanin jama'a

Fifi ta ce:

"Ki nemi wani gidan. Don Allah kada ki wahalar da mu da safen nan."

@literally_rae ta yi martani:

"Yan mata bari na fada maki gakiya, ki cafke wannan damar. Wannan ce hanyar da Allah ke amsar daya daga cikin addu'o'inku. Kada ki dauke wuta musamman idan a Lagas ne."

@Oye4.. ta ce:

"Kin mallaki hankalin kanki sannan kin san abun da kike so."

@Khristopha ta yi martani:

Kara karanta wannan

Cikin Fushi, Fafaroma Francis Ya Yi Martani Kan Kona Kur’ani Da Wasu Mutane Suka Yi a Sweden

"Idan kin shiga rudani, hakan na nufin kina duba yiwuwar amsa tayin, kuma idan kina duba yiwuwar amsawa, hakan na nufin kudin hayar na da tsada sosai kuma ba za ki iya biya ba ba tare da taimakon wani ba. Idan baki da tsayayye kina iya yarda."

Ga wallafar tata a kasa:

Tsadar rayuwa: Diyar biloniya, Hauwa Indimi ta koka kan farashin Tumatir

A wani labari na daban, mun ji cewa diyar biloniya, Hauwa Indimi ta koka kan hauhawan farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a kasar nan.

Duk da kasancewarta diyar biloniya, alamu sun nuna Hauwa ta fara jin radadin tsadar da kayan abinci suka yi a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel