Bayan Shekaru 29: Budurwa Ta Maimaita Rigar Da Mahaifiyarta Ta Sanya a Ranar Aurenta

Bayan Shekaru 29: Budurwa Ta Maimaita Rigar Da Mahaifiyarta Ta Sanya a Ranar Aurenta

  • Wata matashiya yar Najeriya ta yadu a soshiyal midiya saboda yanayin kayan da ta sanya a ranar aurenta
  • Kyakkyawar budurwar mai suna Zubaida wacce ta auri sahibinta ta zabi sanya tufafin da mahaifiyarta ta sa a ranar nata auren
  • Da take sakin hotuna da bidiyoyi, Zubaida ta bayyana dalilinta na yin wallafar a Instagram

Zubaida Rahaman ta kasance kyakkyawar amarya wacce ta sanya kayan amare na alfarma da ya ja hankalin mahalarta bikinta.

Kyakkyawar amaryar ta saki hotuna da bidiyoyin kayan da ta sanya a ranar auren nata sannan ta saki ainahin yadda tufafin yake kafin a yi masa kwaskwarima.

Zubaida ta maimaita kayan auren mahaifiyarta
Bayan Shekaru 29: Budurwa Ta Maimaita Rigar Da Mahaifiyarta Ta Sanya a Ranar Aurenta Hoto: @zubbymoh
Asali: Instagram

Ta rubuta:

"Da nake tasowa, a kodayaushe na kan ji shawa'awar kayan auren mahaifiyata. Bayan an yi mani bako, mahaifiyata ta fada mani cewa ina iya sa kayanta. Ta kan ce mun, "Na siye shi ne a kasar Brazil shekaru kafin na hadu da mahaifinki ko kuma kafin ma na san zan aure shi". Na yanke shawarar gwada kayan, sannan sai duk muka fada tarkon son shi. Ina ta duba zuwa ga yadda za a gyara kayan."

Kara karanta wannan

“Mutane Za Su Taru a Kanmu”: Matashiya Ta Mari Kan Wani Mutum a Motar Haya Don Ganin Me Zai Yi, Bidiyon Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zubaida ta sauya ainahin yadda wuyan rigar ya zo da kuma hannun zuwa na zamani sannan aka rage fadin rigar.

Kalli hotunan a kasa:

Jama'a sun yi martani

krownofhonourcreations:

"Allah ya albarkaceta sosai. Cewa kalan kayan bai sauya ba wani abu ne da ke fito da nagartarsa. Na tayata murna."

_.danniie:

"Ina ganin wannan shawara ce mai kyau, ba kasafai muke gadon kayan aure ba a Najeriya! Shakka babu zai aikata wannan tare da diyata."

ms_ozie:

"Wasu mutanen sun iya adana abubuwa fa...Ni ban ma san inda na jefar da kayan aurena ba."

shop_ponytails:

"Ina son ganin haka...Iyayen Afrika da adana kayansu, kayan kicin da zanuwansu saboda yaransu mata."

Matashiya ta shiga tsaka mai wuya bayan mai gidan da take haya ya nemi su yi ban gishiri na baka manda

Kara karanta wannan

Diyar Biloniya, Hauwa Indimi, Ta Koka Bayan Ta Siya Tumatir Din N8,000, Jama'a Sun Yi Martani

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta bayyanawa jama'a halin da take ciki bayan mai gidansu ya gabatar mata da wata bukata mai ban mamaki.

A cikin wata wallafa da ta yi a shafinta, ta bayyana cewa mai gidansu ya nemi su yi ban gishiri na baki manda a tsakaninsu wato ya nemi su kulla alaka sai ya yafe mata kudin haya idan ta yarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel