Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Ajalin Wani Lauya, Kungiyar Lauyoyi Za Ta Dauki Mataki

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Ajalin Wani Lauya, Kungiyar Lauyoyi Za Ta Dauki Mataki

  • 'Yan bindiga sun kuma hallaka wani lauya mai suna Ahmad Muhammad a karamar hukumar Bangudu da ke jihar Zamfara
  • Kafin rasuwar marigayin, ya rike mukamin Sakataren Jin Dadi na kungiyar lauyoyi ta Najeriya reshen jihar Zamfara
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya ce har zuwa yanzu ba su da wata masaniya akan kisan lauyan da aka yi

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun yi ajalin wani lauya mai suna Ahmad Muhammad Abubakar a gidansa da ke Kotorkoshi a karamar hukumar Bangudu cikin jihar Zamfara.

Marigayin kafin rasuwarsa, shi ne Sakataren Jin Dadi na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), reshen jihar Zamfara.

'Yan Bindiga Sun Yin Ajalin Wani Lauya Bayan Kai Masa Hari A Zamfara
Marigayi Ahmad Muhammad Abubakar. Hoto: TVC News.
Asali: Twitter

Jami'an 'yan ba su ce komai game da kisan ba, amma wani dan uwan marigayin ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Fadar Sarkin Minna Wuta Kuma Yana Ciki, Sun Tafka Ta'adi

'Yan bindigan sun kashe lauyan bayan kai masa hari har cikin gida

Dan uwan marigayin, Aminu Auwal Bangudu ya ce 'yan bindigan sun kai masa hari da safiyar yau Laraba 5 ga watan Yuli kafin tafiya da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"'Yan bindigan sun shiga gidan sai suka ci karo da matarsa, suka kai mata hari sai ta yi ihu, a lokacin ne mijin nata ya fito.
"Sun kai wa mijin hari tare da tafiya da shi, da suka je kan hanya ne suka kashe shi kuma suka jefar da gawarsa.
"Bamu san ta yaya suka kashe shi ba kawai dai mun samu gawarsa a bakin hanya."

Kungiyar lauyoyi a Zamfara sun yi Allah wadai da wannan kisa

Shugaban Kungiyar Lauyoyi reshen jihar, Junaidu Abubakar ya yi Allah wadai da wannan kisa inda ya tabbatar cewa an kashe lauyan, cewar TVC News.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kakaba Wa Dalibai Harshen China A Jami'o'i, Ta Roki Alfarma

A cewarsa:

"Ina tabbatar muku da cewa an kashe shi, sun shiga gidansa amma ba su dauki komai ba, shi kadai suka dauka suka kuma kashe, akwai raunuka na sara a jikinsa."

Ya ce kungiyar za ta yi ganawar gaggawa ganin yadda 'yan bindigan ke yawan kashe musu mambobi a jihar.

Ya kara da cewa:

"Yanzu muka gama jana'izarsa, zamu yi ganawa ta gaggawa, wannan ba shi ne karon farko ba da hakan ke faruwa."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya ce har yanzu ba su da masaniya akan kisan.

Yeriman Bakura Ya Shawarci Tinubu Akan Yin Sulhu Da 'Yan Bindiga

A wani labarin, Sanata Ahmed Sani Yerima ya shawarci Shugaba Tinubu akan yin sulhu da 'yan bindiga.

Yerima ya ce yin sulhun shi ne mafi alkairi kamar yadda aka yi wa tsagerun Neja Delta a baya.

Wannan shawara ta Yerima ta sha suka daga bangarori da dama na kasar ganin yadda aka gwada hakan a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.