'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2

'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2

  • 'Yan fashi sun aikata ta'adi ido na ganin ido a fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, ranar Talata
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun biyo hadimin masarautar tun daga bankin da ya ciro kuɗi har zuwa bakin kofar shiga fada
  • Hukumar 'yan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce tana bin diddigin yadda lamarin ya auku

Minna, Niger State - Wasu 'yan fashi ɗauke da bindigu sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da yammacin ranar Talatan nan da muke ciki.

Yan fashi da makamin sun kutsa kai fadar kuma sun harbi dogarai biyu a harin wanda ake tsammanin sun biyo ɗaya daga cikin hadiman fadar ne tun da farko.

Kofar fadar sarkin Minna.
'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta kawo a rahoton da ta haɗa cewa ɗaya daga cikin masu yi wa fadar hidima da aka aika banki domin ya ciro kuɗi 'yan bindigan suka biyo a wata mota.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mamakon Ruwan Sama Ya Yi Awon Gaba Da Mutane 2 a Birnin Katsina

Bayanai sun nuna cewa Sarki na cikin fada sa'ilin da maharan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane, daga bisani suka yi awon gaba da maƙudan kuɗin da ba'a san iyakarsu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni aka kwantar da dogarai biyu da suka ji raunuka sakamakon harin a babban Asibitin domin kulawa da lafiyarsu.

Ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilin Leadership cewa maharan sun ci ƙarfin 'yan bangan fadar Sarkin yayin musayar wutar da ta auku.

Wane mataki jami'an yan sanda suka ɗauka?

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce maharan ba su shiga cikin fadar ba.

Ya ce wasu gungun 'yan fashi da makami ne suka biyo sawun mai kula da harkokin kuɗin fadar a motar Toyota Camry tun daga bankin da ya je ciro kuɗi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme, Dalibar Da Ta Yi Karyar Cin Maki 362

Kakakin 'yan sandan ya ce:

"A daidai kofar shiga fadar 'yan fashin suka tare shi, kuma sun yi harbe-harbe a iska, daga bisani suka kwace kuɗin ta tsiya a hannunsa suka gudu."

Ya ce a halin yanzun suna karban bayanai daga hadimin Masarautar a hedkwatar 'yan sanda da ke Minna, domin tattara cikakkun bayanan abinda ya faru tun farko.

Dakarun Sojin Sama Sun Kai Samame Kan Mafakar 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno

A wani labarin na daban kuma Sojin saman Najeriya (NAF) sun yi luguden bama-bamai kan mafakar 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Rahoto ya nuna cewa luguden wutan NAF ya halaka mayaƙan ISWAP da yawan gaske kuma ya yi kaca-kaca da wuraren da suke samun mafaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262