Masarautar Zazzau Ta Dakatar Da Hakimi Kan Zargin Lakada Wa Matashi Tsinannen Duka, Ta Gargadi Sauran Dakatai

Masarautar Zazzau Ta Dakatar Da Hakimi Kan Zargin Lakada Wa Matashi Tsinannen Duka, Ta Gargadi Sauran Dakatai

  • Masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna ta dakatar da wani Hakimi bisa zargin daukar mataki da hannunsa na cin zarafi
  • An dakatar da Marafan Yamman Zazzau, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah saboda zargin ya saka an doki wani matashi
  • A martaninshi, Alhaji Mustapha ya ce ya kama matashin ne yana luwadi da wani yaro a bayan gidansa shiyasa ya dauki matakin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Masarautar Zazzau ta dakatar da wani Hakima a majalisar bisa zargin daukar doka a hannunsa.

Hakimin da aka dakatar din, Alhaji Mustapha Ubaidullah ya rasa kujerarsa ta Marafan Yamman Zazzau, bisa tuhume-tuhume.

Masarauta ta dakatar da Hakimi bisa zargin lakadawa matashi duka a Kaduna
Masarautar Zazzau Da Ke Jihar Kaduna. Hoto: Wikipedia.
Asali: UGC

Wannan matakin na zuwa ne bayan koken al'umma daga Unguwar Magajiya da ke birnin Zaria ta jihar Kaduna.

Masarautar ta gargadi sauran dakatai da su guji daukar doka a hannu

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Ana zargin Hakimin da cin zarafin wani matashi mai suna Yusuf Yahaya wanda ba shi da ikon aikata haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da masarautar ta fitar a ranar Talata 4 ga watan Yuli, inda ta ce ta dakatar da shi har sai an gama bincike, Aminiya ta tattaro.

Masarautar ta gargadi masu rike da masarautun gargajiya da su guji daukar doka a hannunsu.

Hakimin ya amince da laifinsa inda ya fadi dalilin dukan matashin

Da ya ke mai da martani akan dakatarwar, Alhaji Mustapha Ubaidullah ya tabbatar da aikata zarginshi da ake inda ya ce ya umarci a doki matashin ne bayan kamashi yana luwadi da wani yaro a jikin gidansa.

Ya ce ya dauki matakin ne don kare martabar kansa da kuma na sarkin Zazzau, inda ya zargi wasu daga cikin ‘yan majalisar Sarkin da hannu wurin kara rura wutar rikicin.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Soke Tsarin Buhari, Ya Hana a Auka CIkin Matsin Tattalin Arziki

A baya masarautar ta sha dakatar da masu sarautar gargajiya a Zazzau, inda Sarki Nuhu Bamalli ya taba dakatar da Ciroman Zazzau daga mukaminsa.

Sarkin Zazzau Ya Tube Rawanin Ciroman Zazzau Bisa Zargin Rashin Biyayya

A wani labarin, Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya tube rawanin Ciroman Zazzau, Alhaji Sa'idu Mai Lafiya.

Sarkin ya sauke shi ne daga mukaminsa bisa zargin rashin biyayya da girmama masarautar.

Wanda aka tuben mai shekaru 84 a duniya ya kasance daga cikin manyan ‘yan majalisar Sarki kuma Dan uwan Sarkin Zazzau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.